An Samu Tashin Hankula da 'Yan Daba Suka Farmaki Magoya Bayan Jam'iyyar NDC
- Wasu da ake zargin ’yan bangar siyasa ne sun kai hari kan magoya bayan NDC a filin jirgin saman Enugu da sakatariyar jam’iyyar
- Bidiyoyi sun nuna yadda magoya bayan jam’iyyar suka riƙa gudun neman tsira yayin da aka riƙa jin harbe-harbe, tare da raunata wani mutum
- Rundunar ’yan sandan Enugu ba ta mayar da martani kan tambayar da aka aika mata ta WhatsApp ba har zuwa lokacin kammala rahoton
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Enugu - An samu tashin hankali a jihar Enugu, bayan wasu da ake zargin ’yan bangar siyasa ne sun kai hari kan magoya bayan jam’iyyar NDC.
'Yan daban na siyasa sun farmaki magoya bayan na jam'iyyar NDC ne a wurare daban-daban na birnin.

Source: Original
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa harin ya fara ne da safiyar ranar Asabar, lokacin da wasu magoya bayan NDC suka yi ƙoƙarin taruwa a filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Akanu Ibiam da ke Emene, amma maharan suka tarwatsa su.

Kara karanta wannan
"Ba cin mutuncin kowa," Gwamna ya ce auna da abiin da za su tallata APC wurin yan Najeriya a 2027
Magoya bayan sun je filin jirgin ne domin tarbar ɗan takarar gwamnan jihar Enugu na jam’iyyar NDC, Chinyeaka Ohaa, wanda ya sauka a filin jirgin kafin fara kamfen ɗin neman zaɓen gwamna na jam’iyyar a ranar Asabar.
An raunata magoyin bayan NDC, an lalata motoci
Bidiyoyin da aka samu sun nuna yadda magoya bayan NDC suka riƙa gudun neman mafaka yayin da maharan ke harbe-harbe lokaci-lokaci.
A wani bidiyo, an ga wani da ake zargin ɗan bangar siyasa ne yana dukan wani magoyin bayan NDC da katako, lamarin da ya raunata shi a gaban sansanin rundunar sojin sama da ke kusa da filin jirgin.
Bidiyon ya kuma nuna wani mutum sanye da kayan soji yana tsaye kusa da wanda ake zargin maharin ne, amma bai yi wani yunƙuri na dakatar da harin ba.
Kafin a kai wa wanda aka raunata harin, an ji wasu magoya bayan NDC suna jan hankalin mutumin sanye da kayan sojin cewa wani ɗan bangar siyasa ya bayyana, amma ya nuna kamar bai damu da abin da ke faruwa ba.
A wani bidiyo daban, an ji wasu magoya bayan NDC suna bayyana ɓacin ransu kan lalata motocinsu da maharan suka yi.
Hakazalika, an samu wani bidiyo da ya nuna motocin da aka fasa gilashinsu.
Wasu magoya bayan jam’iyyar sun zargi jami’an ’yan sanda da sojoji da hannu a harin, amma jaridar ta ce ba ta iya tabbatar da waɗannan zarge-zargen da kanta ba.
An sake kai wa magoya bayan hari a sakatariyar NDC
Bayan magoya bayan NDC sun taru a sakatariyar jam’iyyar da ke Enugu domin fara kamfen ɗin neman zaɓe, waɗanda ake zargin ’yan bangar siyasa ne sun sake kai musu hari a wurin.
Yayin da aka ji harbe-harbe, an ji wasu shugabannin jam’iyyar suna ƙoƙarin kwantar da hankalin magoya bayanta da suka firgita, suna cewa: “Ku tsaya a inda kuke.”
Jaridar ta kuma samu wani bidiyo da ya nuna wasu magoya bayan jam’iyyar suna ficewa daga wurin cikin ruɗani.
Bidiyon ya nuna wasu jami’an ’yan sanda suna harbin waɗanda ake zargin ’yan bangar siyasa ne a kusa da sakatariyar NDC, yayin da magoya bayan jam’iyyar ke gudun neman tsira.
A sakatariyar NDC, inda aka shirya fara kamfen ɗin, kujeru sun watse, rumfunan taro kuma sun lalace, abin da ke nuna yadda harin ya tarwatsa taron siyasar.

Source: Facebook
Rundunar ’yan sanda ba ta mayar da martani ba
Da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan jihar Enugu, Daniel Ndukwe, ya nemi a tuntube shi ta manhajar WhatsApp.
Sai dai har zuwa lokacin kammala rahoton, Ndukwe, wanda ke da muƙamin superintendent of police, bai mayar da martani kan tambayar da aka aika masa ta WhatsApp ba.
NDC ta ba Obi da Kwankwaso dama
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar NDC ta amince Peter Obi, da abokin takararsa, Rabiu Musa Kwankwaso, za su zaɓi wasu manyan jami’an kwamitin yakin neman zabenta.
Shugaban jam’iyyar ya buƙaci ’yan Najeriya su yi watsi da rahotannin da ke ƙoƙarin nuna cewa shugaban jam’iyyar, Sanata Henry Seriake Dickson, bai da cikakken goyon baya ga tikitin Obi da Kwankwaso.
Asali: Legit.ng

