2027: Gwamna Radda Ya Yi Karatun Ta Natsu, Ya Gano Amfanin Sake Zaben Tinubu

2027: Gwamna Radda Ya Yi Karatun Ta Natsu, Ya Gano Amfanin Sake Zaben Tinubu

  • An gudanar da babban taro na jam'iyyar APC a jihar Katsina domin nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Dikko Radda
  • Gwamna Dikko Radda ya yi amfani da taron wajen yin magana kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaben shekarar 2027
  • Dikko Radda ya bayyana tagomashin da za a ci gaba da samu idan har Shugaba Tinubu ya sake samun damar darewa kan kujerar mulkin Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya yi magana kan tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Gwamna Radda ya ce sake zaben Shugaba Tinubu a shekarar 2027 zai ba jihohi da kananan hukumomi damar ci gaba da kai wa al’umma romon dimokuradiyya a yankunansu.

Gwamna Dikko Radda ya fadi amfanin tazarcen Tinubu
Gwamna Dikko Radda a wajen taron jam'iyyar APC a Katsina Hoto: Dr Dikko Umaru Radda
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta ce Radda ya bayar da wannan tabbaci ne a ranar Litinin, 2 ga watan Fabrairun 2026 yayin wani taron jam'iyyar APC da aka shirya a Katsina.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: An bukaci Shugaba Tinubu ya kori ministoci 2 kan wasu zarge zarge

An shirya taron APC a jihar Katsina

An shirya taron ne karkashin jagorancin kungiyar Concerned APC Stakeholders domin goyon bayansa da na Shugaba Bola Tinubu domin samun wa’adi na biyu.

Mahalarta taron sun hada da sanatoci, ’yan majalisar wakilai, ’yan majalisar dokokin jihar Katsina, shugabannin kananan hukumomi, tsofaffin gwamnonin jihar Alhaji Aminu Masari da Alhaji Ibrahim Shema.

Sauran sun hada da dattawan Katsina, da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar APC tare da bayyana goyon bayansu ga Tinubu da Radda.

Me Radda ya ce kan Shugaba Tinubu?

Gwamna Radda ya ce tun bayan da Shugaba Tinubu ya hau mulki, yana sakin kudade kai tsaye ga kananan hukumomi, lamarin da ke ba su damar bunkasa yankunansu, jaridar People Gazette ta kawo labarin.

"Wasu mutane na fadin abubuwa da dama kan gwamnatocin da suka gabata, har da ta Shugaba Tinubu. Amma abin da ya fi damunmu shi ne abin da zai kawo ci gaba ga kasa."

Kara karanta wannan

APC ta kara karfi, Shettima ya karbi gwamnan da ya shiga jam'iyyar a hukumance

“Mutanen Katsina suna farin ciki da abin da muke yi. Amma muna iya yin hakan ne saboda kudaden da shugaban kasa ke sakar wa jihohi da kananan hukumomi."
“Wannan goyon baya zai kara mana kwarin gwiwa domin mu kara yi wa jama’a aiki. Ina ba ku tabbacin ba za mu ba ku kunya ba."

- Gwamna Dikko Umaru Radda

Gwamna Radda ya goyi bayan tazarcen Tinubu
Gwamna Dikko Umaru Radda tare da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Source: Facebook

Meyasa aka goyi bayan Tinubu, Radda

Tun da fari, shugaban kungiyar Concerned APC Stakeholders, Sanata Ibrahim Ida, ya ce sun yanke shawarar goyon bayan ne sakamakon kyakkyawan shugabanci da Tinubu da Radda suka nuna.

Ya ce jajircewarsu ta haifar da ingantuwar rayuwar al’umma cikin shekaru biyu da rabi kacal kan karaga.

Don haka, Ida ya bukaci masu kada kuri’a da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin sake zaben Tinubu da Radda a babban zaben 2027.

Tinubu ya shiga tsakani a rikicin Rivers

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake shiga tsakani a rikicin siyasar jihar Rivers.

Mai girma Bola Tinubu ya nuna damuwa kan yadda rikicin ke kokarin tsayar da harkokin mulki, inda ya ce ba zai lamunci hakan ba.

Shugaba Tinubu ya ba da umarnin a dakatar da yunkurin tsige Gwamna Siminalayi Fubara daga kan mukaminsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng