Rigimar ADC Ta Ki Karewa, 'Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Ce za a Wargaza Lissafin 'Yan Hadaka
- Tsohon dan takarar Shugaban Kasa a ADC, Dumebi Kachikwu ya bayyana takaicin yadda INEC ta mika jagorancin jam'iyya ga David Mark
- Yana ganin abin da INEC ta yi ya saba doka, ganin cewa yanzu haka batun shugabancin jam'iyya yana gaban kotu ana fafata wa
- Kachikwu ya ce David Mark da abokansa, tsofaffin 'yan siyasa ne da suka dade suna gaza wa, saboda haka kuskure ne a bi su
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Dumebi Kachikwu, dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 karkashin ADC, ya bayyana rashin amincewa da matakin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) kan shugabancin jam'iyya.
Tsohon dan takarar ya fusata ne bayan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta tabbatar da jagorancin ADC ga 'yan hadakar adawa karkashin David Mark.

Source: Twitter
Kachikwu ya caccaki hukumar INEC
The Cable ta wallafa cewa Dumebi Kachikwu na ganin cewa INEC ta yi rashin gaskiya ne da rashin kishin kasa da ta amince da David Mark da Aregbesola kan jagorancin ADC.
Ya ce:
“Abin da muka gani daga INEC jiya wani sakaci ne daga shugaban hukumar wanda yake kan hanyarsa ta barin ofis."
Kachikwu ya ce akwai shari’a da ke gudana a kotu game da rikicin shugabancin ADC, don haka bai dace INEC ta dauki mataki ba kafin kotu ta yanke hukunci.

Source: Twitter
Ya kara da cewa:
“Doka ta ce idan akwai kara a gaban kotu, kada a dauki wani mataki da zai iya shafar hukuncin da za a yank.”
Ya bayyana cewa shari’ar rikicin jagoranci tsakaninsa da bangaren David Mark za ta ci gaba a kotu a watan gobe.
'Ba za su iya ba,' Kachikwu ya fusata
Kachikwu ya bayyana cewa mutanen da ke goyon bayan David Mark sun saba cin gajiyar siyasa ne kawai, kuma ba su abin yi sai kokarin dawo da kansu mulkin Najeriya.
Ya ce:
“Wadannan mutanen ba za su iya tsayawa a yi wa jama'a aiki ba. Suna so ne su dawo don su ci gaba da kula da kawunansu da abokansu."
Ya kara da cewa masu ruwa da tsaki da ke mara wa Mark baya ba su da cikakken hangen nesa da zai ceto Najeriya daga halin da take ciki.
A kalaman Kachikwu:
“Shin a kasar da ke da sama da mutane miliyan 200, sai dai mu dogara da ‘yan siyasa ‘yan da suka gaza a baya? Wannan ba zai yiwu ba."
Sabon rikici ya danno jam'iyyar ADC
A baya, mun wallafa cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a zaɓen 2023, Dumebi Kachikwu, ya bayyana rashin amincewarsa da sabon jagorancin jam’iyyar.
Kachikwu ya zargi wasu manyan ‘yan adawa da shiga jam’iyyar ta hanyar da bai dace ba, yana cewa wannan hanya da suka bi ta saba doka ce kuma ba yi fatali da tsarin dimokuradiyya.
Ya kara da cewa wa'adin Ralph Nwosu da ya mika ADC ga 'yan adawa ya jima da kare wa, saboda haka sun karbi jam'iyya daga hannun wanda ba shi jagoranta ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

