'Kwankwaso ba Zai Goyi bayan Tinubu a Zaben 2027 ba,' Buba Galadima Ya Kawo Dalilai
- Buba Galadima ya bayyana cewa kila Sanata Rabiu Kwankwaso ba zai haɗa kai da Shugaba Bola Tinubu da APC a zaben 2027 ba
- Ya ce gwamnatin Tinubu tana amfani da ’yan sanda da kotuna wajen goyon bayan Aminu Ado Bayero duk da an tsige shi daga sarauta
- Buba ya yi ikirari cewa NNPP ce za ta yanke shawarar wanda zai zama shugaban kasa a 2027, tare da jaddada ƙarfin Kwankwaso
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Buba Galadima, babban jigo a jam’iyyar NNPP, ya karyata yiwuwar babban ɗan siyasar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya haɗa kai da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Buba Galadima ya ce gwamnatin Tinubu ta yi wa Kwankwaso da NNPP rashin adalci a Kano ta hanyar goyon bayan tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, duk da cewa Gwamna Abba Kabir ya tsige shi.

Kara karanta wannan
APC: Duk da lashe kujera, Ministan Tinubu ya roki INEC ta soke nasarar NNPP a Kano

Asali: Twitter
Laifin da Tinubu ya yi wa Kwankwaso, NNPP
Fitaccen dan siyasar ya amayar da ta cikinsa ne a shirin 'Siyasa a yau' na gidan talabijin din Channels a ranar Litinin, 18 ga Agusta, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A lokacin hirar, Buba Galadima ya ce:
“Ta yaya za a ce Kwankwaso zai kulla kawance da APC bayan duk irin abin da suke yi mana a Kano? Ɗora sarakuna biyu a gari guda?
"Akwai sarkin gwamnatin tarayya, akwai sarkin gwamnatin jiha. Amma abin tambayar shi ne, wanene ke da hurumin naɗa sarakuna da biyansu albashi?
“Sun ba nasu sarkin kusan motoci 40 na Hilux cike da ’yan sanda suna tsaronsa, an tara masa 'yan sanda yayin da a wasu yankunan Kano ake kashe mutane, ana kwace wayoyinsu. Shin ba su da kunya ne?”
‘NNPP ce za ta zaɓi shugaban ƙasa a 2027’
Buba Galadima ya yi ikirari cewa jam'iyyar NNPP ce za ta yanke shawarar wanda zai zama shugaban Najeriya a 2027.
'Dan siyasar ya ce:
“Mu ne za mu tantance wanda zai zama shugaban ƙasar Najeriya a 2027.”
Masarautar Kano dai ta kasance cikin rikice-rikice na shekaru 10 inda bangaren Bayero da Sanusi ke fafatawa da juna kan sarautar.
A shekarar 2014, Sarki Muhammadu Sanusi II ya gaji mahaifin Aminu Ado Bayero, watau marigayi Sarki Ado Bayero.
Amma Dr. Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan Kano na wancan lokaci ya tsige Sanusi II, ya maye gurbinsa da Aminu Bayero.
Sai dai, a shekarar farko ta mulkin Gwamna Abba Kabir Yusuf, aka tsige Aminu Bayero, aka dawo da Sanusi kan karagar mulki.
'Tinubu ne ya nemi a nada Sanusi' - Galadima
Wannan lamari ya jawo rigimar sarauta mai zafi a Kano, inda kotuna daban daban suka yanke hukunci mabanbanta kan wanda ya fi cancantar zama sarkin Kano.
Yayin da gwamnatin Kano ta dage cewa Sanusi II ne halastaccen sarki, a bangare daya kuma, Aminu Bayero ya dage cewa shi ne sarki, kuma har yanzu yana zaman fada.
A kan wannan gabar, Buba Galadima ya ce kotun tarayya ba ta da ikon yanke hukunci a kan harkar sarauta.
“Ai tun da fari, Shugaba Tinubu ne ya nemi a naɗa Sanusi sarki? Ya fito ya ƙaryata maganata idan ba shi ba ne, zan kawo hujjoji."
- Buba Galadima.

Asali: Facebook
Akwai hannun gwamnatin tarayya a nadin Aminu Ado
Babban jigon NNPP ɗin ya zargi gwamnatin tarayya da amfani da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro wajen tayar da hankula a Kano.
Ya ce gwamnatin tarayya na goyon bayan Aminu Ado Bayero, saboda suna ganin zai taimaka musu a zaɓen 2027, amma ya jaddada cewa babu wani sarkin Kano da ya taɓa tantance wanda zai zama shugaban Najeriya.
Buba ya ƙara da cewa Kwankwaso bai taɓa gaya masa zai mara wa APC ko Tinubu baya a zaɓen 2027 ba.
“Bari wani ya fito ya ce ya gana da Kwankwaso, ya shawo kansa, ya roƙe shi ko ya tilasta masa ya shiga APC. Idan har hakan za ta faru, to lallai zan sani.

Kara karanta wannan
'Za mu more': An faɗi dalilai da ke nuna Jonathan ne mafi dacewa da bukatun Arewa
“Shi ne ɗan siyasa mafi ƙarfi a ƙasar nan a yau, domin ya kalubalanci APC ya kuma lallasa su a jihar Kano."
- Buba Galadima.
Matsayar NNPP kan hadakarsu Atiku
A wani labarin, mun ruwaito cewa, babban jigon NNPP, Alhaji Buba Galadima, ya yi magana game da sauya sheƙar da wasu ƴan siyasa suke yi zuwa SDP.
Buba Galadima ya ce babu wani abin mamaki dangane da rashin ganin jiga-jigan NNPP suna komawa SDP, domin a cewarsa, jam’iyyar wani reshe ne na APC.
Jawabin shi ya biyo baysan kiran da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi na cewa ya shugabannin adawa su haɗu a SDP domin su ƙwace mulki daga APC a 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng