Abba Ya Tabbatar da Korar Aminu Ado Bayero, Ya Sanya Hannu a Dokar da Ta Rusa Su

Abba Ya Tabbatar da Korar Aminu Ado Bayero, Ya Sanya Hannu a Dokar da Ta Rusa Su

  • A karshe, Gwamna Abba Kabir ya amince da dokar rusa masarautu a jihar Kano inda ya sanya hannu domin tabbatar da ita
  • Hakan ya tabbatar da korar Aminu Ado Bayero daga kujerar sarautar jihar Kano da sauran sarakuna guda hudu da abin ya shafa
  • Wannan na zuwa ne awanni kadan bayan majalisar dokokin jihar ta amince da rusa masarautun guda biyar a yau Alhamis 23 ga watan Mayu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya sanya hannu kan dokar da ta rusa masarautun jihar a yau Alhamis 23 ga watan Mayu.

Gwamnan ya sanya hannun ne a yau Alhamis, 23 ga watan Mayu bayan mika masa takarda mai dauke da dokar a gidan gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan

Dawo-Dawo: An sanar da sabon Sarkin Kano, Sanusi II ya zama sarki a karo na biyu

Abba Kabir ya sanya hannu a dokar rusa masarautun Kano
Gwamna Abba Kabir ya sanya hannu a dokar da majalisar dokoki a Kano ta yi. Hoto: Abba Kabir Yusufu, Sanusi Lamido Sanusi.
Asali: Facebook

Abba Kabir ya sanya hannu a doka

Wannan na kunshe ne a cikin wani faifan bidiyo da hadimin Sanata Rabiu Kwankwaso, Ibrahim Adam ya wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rattaba hannu a dokar shi ya sake tabbatar da rushe masarautu biyar da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro lokacin mulkinsa a jihar.

Hakan ya biyo bayan ƙirƙirar masarautun da Abdullahi Ganduje ya yi a watan Disambar 2019 lokacin yana mukin jihar.

Masu nadin sabon Sarki suna gidan gwamnati

Har ila yau, mun ruwaito muku cewa masu nadin sabon Sarki sun isa gidan gwamnatin jihar Kano domin fara shirye-shirye.

Hakan ya biyo bayan rusa masarautun jihar guda biyar da Majalisar dokokin jihar ta yi a yau Alhamis 23 ga watan Mayu.

Daga cikinsu akwai Madakin Kano da hakimin Dawakin-Tofa da Yusuf Nabahani da Makaman Kano sauransu.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya sa labule da 'yan majalisamasu nada Sarki a Kano, bayanai sun fito

Abba ya dawo da Sanusi kujerarsa

A wani labarin, kun ji cewa an sanar da Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon sarkin Kano shekaru hudu bayan tsige shi.

Wannan na zuwa ne bayan da majalisar dokokin jihar ta tabbatar hade masarautun jihar guda biyar da tsige dukkan masu rike da mukaman.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ne ya ayyana Malam Muhammadu Sunusi II a matsayin sarkin Kano a yau Alhamis 23 ga watan Mayu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel