Ganduje Ya Sauka, Yilwatda Ya Hau: Jerin Shugabannin APC 9 daga 2013 zuwa 2025
- Tarihin APC ba zai taba cika ba sai an waiwaya shekarar 2013, lokacin da jam'iyyun adawa uku; ACN, CPC da ANPP suka hade waje daya
- A 2015, wannan hadakar ta haifar da ɗa mai ido, APC ta kawo karshen mulkin PDP na shekaru 16, nasarar da za a jingawa shugabanninta
- Yayin da Nentawe Yilwatda ya zama shugaban APC na kasa, Legit Hausa ta jero dukkanin shugabannin jam'iyyar daga 2013 zuwa 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Jam’iyyar APC na daga cikin manyan jam’iyyu da suka taka rawa matuka a siyasar Najeriya tun bayan kafuwarta a shekarar 2013.
Legit Hausa ta tattaro cewa an kafa jam’iyyar ne bayan hadewar manyan jam’iyyun adawa guda uku: ACN,CPC, da kuma jam'iyyar ANPP.

Asali: Twitter
Kafuwar jam’iyyar ta biyo bayan bukatar dunkulewa da ceto Najeriya daga mulkin jam’iyyar PDP da ke kan karagar mulki tun daga 1999, a cewar wani bincike a ResearchGate.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta samu nasarar kafa gwamnati a matakin tarayya a shekarar 2015, lokacin da Muhammadu Buhari ya lashe zaben shugaban kasa, abin da ya zamewa jam’iyyar tarihi.
A wancan lokaci, APC ya samu gudumuwa daga cikin wasu da suka balle daga jam'iyyar PDP.
Jerin shugabannin APC daga 2013-2025
Tun daga wancan lokaci, jam’iyyar ta sha samun sababbin shugabanni da ma sauye-sauye masu muhimmanci, ciki har da rikice-rikice na cikin gida.
Ga jerin shugabannin jam’iyyar APC daga 2013 zuwa yanzu (Yuli, 2025):
1. Chief Bisi Akande (2013 – 2014)
Bisi Akande, tsohon gwamnan jihar Osun, ya rike shugabancin APC a matsayin shugaban rikon kwarya lokacin da aka kafa jam’iyyar.
Shi ne ya jagoranci tattaunawar hadin kai tsakanin jam’iyyun ACN, CPC, da ANPP. A karkashinsa ne aka samu daidaito da cimma nasarar kafa jam’iyyar a hukumance.
2. Chief John Odigie Oyegun (2014 – 2018)
Oyegun shi ne shugaban jam’iyyar na farko bayan jam’iyyar ta samu rajista daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
A lokacin mulkinsa ne APC ta samu nasarar lashe zaben shugaban kasa a 2015 da wasu kujerun majalisun tarayya.
Oyegun ya fito daga jihar Edo kuma ya bar mukamin bayan wa’adi guda, kamar yadda Legit Hausa ta rahoto jawabinsa na bankwana mai ratsa zuciya.
3. Adams Oshiomhole (2018 – 2020)
Adams Oshiomhole ya kasance tsohon shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC) sannan tsohon gwamnan Edo.
Oshiomhole ya shahara da tsauraran matakai a yunkurin tsaftace jam’iyyar, sai dai mulkinsa ya haddasa rikice-rikice, ciki har da rabuwar kawuna da wasu gwamnoni.
Hakan ya sa aka dakatar da shi daga shugabanci a 2020. Mun ruwaito cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin dakatar da Oshiomhole.
4. Mai Mala Buni (2020 – 2022)
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya rike jam’iyyar APC a matsayin shugaban kwamitin rikon kwarya.
A karkashinsa ne aka samu shigar sababbin mambobi da kuma aiwatar da kwaskwarima a cikin APC domin farfado da ita da karin hadin kai.
Duk da haka, a Maris din 2022 muka ruwaito cewa marigayi Muhammadu Buhari (shugaban kasa na wancan lokaci) ya amince da tsige Buni kan kin gudanar da zaben jam'iyyar.
5. Sanata Abdullahi Adamu (2022 – Yuli 2023)
Sanata Abdullahi Adamu ya kasance tsohon gwamnan Nasarawa kuma dajjito a majalisar dattawa.
A karshen mulkinsa ya bayyana cewa bai goyi bayan Bola Tinubu a lokacin zaben fidda gwanin APC ba.
Ya ajiye mukaminsa a Yuli 2023 kuma ya fice daga siyasa gaba daya a watan Disamba, kamar yadda muka ruwaito lokacin da ya sanar da ritayarsa.
6. Sanata Abubakar Kyari (Yuli – Agusta 2023)
Sanata Abubakar Kyari, tsohon dan majalisar dattawa daga Borno, ya hau matsayin kujerar shugaban rikon kwarya bayan murabus din Adamu.
A matsayinsa na mataimakin shugaban jam’iyya na Arewa, ya jagoranci taron kwamitin zartarwa (NWC) a Abuja a ranar 17 ga Yuli 2023.

Asali: Twitter
7. Abdullahi Ganduje (Agusta 2023 – Yuni 2025)
Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kasance tsohon gwamnan Kano wanda ya taba rike mukamin har sau biyu a jere.
Ganduje ya jagoranci jam'iyyar APC a lokacin da aka fuskanci kalubale da gyare-gyare a cikin jam’iyyar.
Mun ruwaito cewa Ganduje ya ajiye mukaminsa a ranar 27 ga Yuni 2025 bisa dalilan lafiya kamar yadda wata takarda ta nuna.
8. Hon. Ali Bukar Dalori (Yuni – Yuli 2025)
Mataimakin shugaban jam’iyya na arewa, Hon. Ali Bukar Dalori, ya maye gurbin Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban rikon kwarya.
An tabbatar da sauyin ne a wani taron jagororin jam’iyyar a Abuja bayan Ganduje ya ajiye aiki, kamar yadda muka ruwaito.
9. Farfesa Nentawe Yilwatda (Yuli 2025 – yanzu)
Legit Hausa ta rahoto cewa, Farfesa Nentawe Yilwatda, wanda ya kasance ministan jin kai na Najeriya, shi ne shugaban jam’iyyar na yanzu.

Kara karanta wannan
'Zai dawo': PDP ta yi watsi da ficewar Atiku, ta faɗi babban abin da zai dawo da shi
An sanar da nadinsa a ranar 24 ga Yuli 2025 a matsayin cikakken shugaban jam’iyyar na kasa. Farfesa ne a fannin Injiniya kuma yana da kwarewa a mulki da harkokin jam’iyya.
Jam’iyyar APC ta fuskanci sauye-sauye da dama a shugabancinta cikin shekaru 12 da suka gabata.
Sabon shugaban jam’iyyar na fuskantar kalubalen hadin kai, gyaran gida da kuma shiryawa babban zaben 2027.
Yilwatda ya daukarwa APC wasu alkawura
Tun da fari, mun ruwaito cewa, sabon shugaban APC na ƙasa, Yilwatda Nentawe, ya ce zai haɗa kai da kowa domin faɗaɗa jam’iyyar a fadin Najeriya.
Farfesa Nentawe ya bayyana hakan ne a jawabin karɓar mukami yayin taron NEC na jam’iyyar APC da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis.
Gwamna Hope Uzodimma ne ya gabatar da kudirin zabar Nentawe daga Arewa ta Tsakiya, wanda Kakakin Majalisa, Tajudeen Abbas ya mara wa baya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng