Gangamin APC: Oyegun ya yi jawaban bankwana ma su ratsa jiki

Gangamin APC: Oyegun ya yi jawaban bankwana ma su ratsa jiki

Mun samu rahoton cewa shugaban jam'iyyar APC mai murabus, Cif John Odigie-Oyegun, ya yi bankwana da shugabannin jam'iyyar sa yayin gangamin ta da ta gudanar a yau Asabar a babban birnin kasar nan na Abuja.

Oyegun cikin jawaban sa na karshe da ya gabatar kan kujerar shugabancin jam'iyyar ga wakilan ta ya gargade su akan kada su gaza wajen ci gaba da goyon bayan jama'iyyar dari bisa dari.

Gangamin APC: Oyegun ya yi jawaban bankwana ma su ratsa jiki

Gangamin APC: Oyegun ya yi jawaban bankwana ma su ratsa jiki

Ya kuma mika godiyar sa gami da yabo ga jagororin da suka kafa jam'iyyar da suka jajirce kan juriya da hakuri yayin da matsanantan lokuta da jam'iyyar ta fuskanta.

DUBA WANNAN: 'Yan Majalisar mu ba su cancanci mu sake zaben su ba - Shugabannin Neja Delta

A yayin haka kuma, shugaban kwamitin shirya gangamin jam'iyyar, Abubakar Badaru ya bayyana cewa, ko shakka babu an samu rabuwar kawuna cikin mambobi jam'iyyar dangane da takarar mukamai daban-daban.

Sai dai ya bayyana gamsuwar sa tare da amince da cewar matsalolin da jam'iyyar ke fuskanta a halin yanzu za su zamto tarihi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel