Malami da Jerin Ministocin Buhari da Suka Fice daga APC, Suka Shiga Haɗakar ADC

Malami da Jerin Ministocin Buhari da Suka Fice daga APC, Suka Shiga Haɗakar ADC

Jam’iyyar haɗaka watau ADC da Atiku Abubakar ke jagoranta na ƙara ƙarfi a shirinta na kwace mulki daga hannun Shugaba Tinubu da jam’iyyar APC a zaɓen 2027.

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Tsoffin ministoci da suka yi aiki a gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari sun fara ficewa daga APC mai mulki zuwa ADC.

Tsofaffin ministoci a Gwamnatin Najeriya.
Amaechi da wasu ministocin Buhari sun shiga ADC Hoto: Rauf Aregbesola, Rt. Hon. Chibuike R. Amaechi, Abubakar Malami SAN
Source: Facebook

Tribune ta rahoto cewa Akalla tsofaffin ministoci huɗu sun fara sukar APC da kuma wanda ya gaji Buhari, watau Bola Tinubu kan halin kuncin da ake ciki.

Uku daga cikin waɗannan tsofaffin ministoci ba wai kawai sun fice daga APC ba ne, sun shiga ƙungiyar haɗaka da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ke jagoranta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwanan nan kungiyar haɗakar ta amince da jam’iyyar ADC a matsayin dandalin siyasarta gabanin babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

"Akwai jan aiki a gabanmu," Tsohon aminin Tinubu ya hango abin da zai karya APC a 2027

Legit Hausa ta tattaro muku ministoci huɗu na Muhammadu Buhari da suka tattara kayansu suka bar APC zuwa ADC. Ga su kamar haka.

1. Rauf Aregbesola

Rauf Aregbesola, ya kasance tsohon gwamnan jihar Osun kuma tsohon Ministan Harkokin Cikin Gidax wanda ya yi aiki a lokacin mulkin Muhammadu Buhari.

Aregbesola, wanda a baya ya kasance aminin Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya fara samun matsala da tsohon gwamnan jihar Legas ne tun kafin zaɓen gwamnan Osun na 2022.

Tsohon ministan hadida Tinubu sun fara samun matsala ne lokacin da ya shawarci Gwamnan Osun na wancan lokacin, Gboyega Oyetola, da ya haƙura da neman wa’adin biyu ba.

Tsohon ministan cikin gida, Rauf Aregbesola.
Rauf Aregbesola ya karbi muƙamin sakataren rikon kwarya na ADC Hoto: Rauf Aregbesola
Source: Facebook

Sai dai Tinubu bai aminta da wannan shawara ta Rauf Aregbesola, wanda daga ƙarshe kuma Oyetola ya sha ƙasa a zaben gwamnan da aka yi a Osun.

Wannan rashin nasara ta Oyetola ta zamo farkon rikici tsakanin Aregbesola da Shugaba Tinubu.

A wasu kalamai da ya yi kafin zaɓen, Aregbesola ya ce Tinubu bai so abin da ya yi wa tsohon gwamnan Legas, Akinwunmi Ambode, ya faru da dan uwansa, Oyetola.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Jiga jigai 3 sun nemi ruguza haɗaƙar Atiku, Obi da yan haɗaka a ADC

A halin yanzu kuma, Rauf Aregbesola ya tattara kayansa ya bar APC kuma ya karɓi matsayin sakataren riƙon kwarya na jam'iyyar ADC kamar yadda ya wallafa a shafin X.

2. Abubakar Malami

Abubakar Malami, tsohon Antoni Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari'a a lokacin mulkin Buhari, ya fice daga jam'iyyar APC zuwa ADC a ranar Laraba, 2 ga Yuli.

Tsohon ministan ya bayyana sauya shekar tasa ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.

Abubakar Malami.
Tsohon Antoni Janar, Abubakar Malami ya bi sahun jiga-jigam da ke shiga ADC Hoto: Abubakar Malami SAN
Source: Twitter

Abubakar Malami ya ce ba wai ya ɗauki wannan matakin saboda fusata ko fushin tsohuwar jam’iyyarsa ba ne, sai dai saboda ƙaunar da yake yi wa jihar Kebbi da Najeriya gaba ɗaya.

A cikin saƙon, Malami ya sanar da murabus dinsa daga jam’iyyar APC mai mulki, yana mai cewa, "zubar jini ya yawaita a Najeriya."

Ya bayyana rashin tsaro da ke addabar Arewacin Najeriya kamar garkuwa da mutane, ‘yan bindiga da ta’addanci, yana mai cewa wadannan abubuwa sun zama ruwan dare gama gari.

3. Rotimi Amaechi

Rotimi Amaechi, tsohon Ministan Sufuri a gwamnatin Buhari, ya yi murabus daga jam’iyyar APC mai mulki ya kuma koma jam’iyyar ADC.

Kara karanta wannan

Yadda jagororin APC suka ki tarbar Kashim Shettima a Kano bayan Ganduje ya yi murabus

Amaechi, wanda ya taɓa zama gwamnan jihar Rivers har sau biyu, ya ce Najeriya ta faɗa mawuyacin hali kuma tana bukatar sauyi gaba ɗaya.

Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi.
Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya shiga jerin masu neman takara a ADC Hoto: Rt. Hon. Chibuike R. Amaechi
Source: Facebook

Tsohon gwamnan ya zargi gwamnatin tarayya karkashin jagorancin APC da kuma Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da haɗa kai domin yin maguɗin zaɓe a 2027.

A wata hira da ya yi da Channels tv, Amaechi ya bayyana sha'awarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027, ya ce shekaru huɗi zai yi ya sauka.

4. Hadi Sirika

Ana zargin tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama a ƙarƙashin mulkin Buhari, Hadi Sirika ya fice daga jam’iyyar APC zuwa ADC.

Duk da ya fito ya musanta labarin da cewa yana nan tare da Muhammadu Buhari a APC, amma ganinsa a taron kaddamar da ADC a matsayin jam'iyyar haɗaka ya nuna alamun ya sauya sheka.

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika.
Ana zargin Hadi Sirika ya bi sahun ministocin Buhari da suka shiga ADC Hoto: Hadi Sirika
Source: Facebook

Sirika yana fuskantar shari’a kan zargin ba da kwangiloli da suka kai darajar biliyoyin Gaira ga ‘yan uwansa.

EFCC ta zarge shi da rashin aiwatar da kwangilolin bayan an raba su gida biyu. Ana zargin an ba ‘yarsa da kamfanin mijinta kwangilar da ta kai kusan Naira biliyan 3.7.

Kara karanta wannan

Yaƴan jagororin ADC da ke cikin jam'iyyun APC da PDP a yau

Aregbesola ya hango faɗuwar APC

A wani rahoton kun ji cewa tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ya ce ADC za ta iya kawo ƙarshen mulkin APC idan ƴan adawa suka haɗa kai.

Aregbesola ya ce jam’iyyar ADC na gina wani babban ƙawance da ke haɗa ’yan Najeriya masu kishin ƙasa don kalubalantar gwamnatin Bola Tinubu.

Ya kuma ja kunnen mambobin haɗaka da su shiryawa farfaganda daga APC, wadda ya ce za ta yi duk mai yiwuwa wajen tarwatsa wannan haɗaka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262