'Yar Buba Galadima Ta Tsorata Tinubu kan 'Yan Arewa a Zaben 2027
- Zainab Buba Galadima ta ce Bola Tinubu zai fuskanci gagarumin kalubale daga Arewacin Najeriya a zaben 2027
- Ta ce watakila shugaba Bola Tinubu ba zai samu fiye da kashi 30 na kuri’un Arewa ba saboda rashin gamsuwa
- Zainab ta bayyana cewa haɗakar ‘yan adawa da ƙin jin daɗin jama’a na nuna cewa wannan zabe zai fi na 2023 wahala
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja - Zainab Galadima, ‘yar Buba Galadima wanda fitaccen jigo ne a jam’iyyar NNPP, ta bayyana cewa zaben 2027 zai kasance mafi tsauri da wahala ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Zainab Buba Galadima ta ce Bola Tinubu zai fuskanci kalubale mafi girma tun daga lokacin da ya fara harkar siyasa.

Source: Facebook
Ta bayyana haka ne yayin hira a wani shiri na ma'aikacin Channels Television, inda ta ce rashin jin daɗin jama’a musamman a Arewa na kara yi wa Tinubu tarnaki a tunkarar zabe mai zuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zainab Buba ta tsorata Tinubu da 'yan Arewa
Zainab ta bayyana cewa bisa ga ra’ayoyin da take samu daga yankin Arewa, ba za a iya cewa mutane na jin daɗin mulkin Tinubu ba.
Rahoton The Cable ya nuna cewa Zainab Buba Galadima ta yi hasashen cewa watakila ba zai samu fiye da kashi 30 na kuri’un yankin ba.
Ta ce:
“Gaskiya, ra’ayoyin mutane da nake ji daga Arewa ba su da kyau game da Tinubu. Ba lallai ya samu fiye da kashi 30 na kuri’un yankin ba.”
Ta ƙara da cewa:
“Zaben 2027 zai fi na 2023 wahala a gare shi. Wannan ne zai zama mafi wuya a cikin duk gwagwarmayar siyasar da ya taɓa shiga.”
Hadakar 'yan adawa na ƙara ƙarfafuwa
Zainab ta nuna damuwa kan yadda jama’a da dama ke nuna goyon baya ga sabuwar haɗakar jam’iyyun adawa da suka amince da amfani da jam’iyyar ADC a matsayin sabon dandali.
A cewarta, ko da yake bata gama fahimtar tsarin haɗakar ba, amma kowa na iya gane cewa akwai buƙatar Tinubu da magoya bayansa su farka.
Hadakar ta ƙunshi fitattun ’yan adawa da suka haɗa da Atiku Abubakar, Peter Obi da tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark, inda suke shirin fuskantar APC da Tinubu a 2027.

Source: Twitter
Zainab Buba Galadima ta taɓa aiki a matsayin mai ba mataimakin shugaban kasa shawara a kan ayyukan SDGs a lokacin mulkin Muhammadu Buhari.
Buba Galadima ya yi magana kan 2027
A wani rahoton, kun ji cewa jigo a NNPP, Buba Galadima ya ce Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne ya fi cancanta ya shugabanci Najeriya a 2027.
Buba Galadima ya bayyana haka ne yayin da ake hira da shi game da rade radin sauya shekar Rabiu Kwankwaso.
A yayin hirar, Buba Galadima ya ce Rabiu Kwankwaso ba zai sauya sheka ba duk da yawan kiran da APC da PDP ke masa ya koma cikinsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

