ADA: Atiku Ya Gana da 'Yan Kanyywood, 'Yan Siyasar Arewa kan Sabuwar Tafiya
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa an kusa kaddamar da wani babban kawance na ‘yan adawa domin farfaɗo da Najeriya
- Wani gungun masu ruwa da tsaki daga Arewa maso Yamma sun shaida masa cewa suna shirye-shiryen goyon bayan wannan kawance a zaben 2027
- Atiku ya jaddada cewa Najeriya na bukatar canji mai ma’ana, kuma wannan ƙawance na da ƙwarewar da za zai iya fuskantar matsalolin ƙasa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya gana da 'yan Kannywood da wasu 'yan siyasa.
Yayin da ake shirin zaben 2027, Atiku Abubakar ya bayyana cewa an kusa bayyana wani sabon kawancen ‘yan adawa da nufin gyara Najeriya.

Kara karanta wannan
ADA: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da sabuwar jam'iyyarsu Atiku da El Rufai

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanan Atiku Abubakar ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya yi bayani ne yayin da ya karɓi baƙuncin wata tawaga daga ƙungiyar masu harkar kafafen sada zumunta na Arewa maso Yamma.
Tawagar, ƙarƙashin jagorancin Dr Aslam Aliyu daga Zamfara, ta fito daga ƙungiyoyi daban-daban ciki har da masana’antar Kannywood da Zamfara Top 10.
Atiku Abubakar ya ce suna da niyyar gyara kasa
A cewar Atiku, wannan kawance ba wasa ba ne, domin yana da nufin gyara da sake gina ƙasa ta hanyar amsa ƙorafe-ƙorafen da jama’a ke yi game da matsalolin da suke fuskanta.
Ya jaddada cewa burin kawancen shi ne ceto Najeriya daga matsalolin da suka dabaibaye ta, musamman ta fuskar rashin tsaro, tattalin arziki da shugabanci mara hangen nesa.
Atiku Abubakar ya nuna farin cikinsa da ganin matasa da masu tasiri a kafafen sada zumunta suna taka rawa wajen wayar da kai da shirye-shiryen sauya gwamnati a 2027.
Bakin Atiku sun yi nadamar zaben Tinubu
A cikin jawabansa, Atiku ya ce wasu daga cikin mambobin tawagar sun amsa cewa sun taka rawa a samar da gwamnati mai ci, wato gwamnatin Tinubu, kuma sun nuna nadama matuƙa.
Sun shaida cewa gwamnatin yanzu ta gaza kuma ta kasa tafiyar da mulki yadda ya kamata, lamarin da ya sanya su yanke shawarar marawa sabon kawancen baya.

Source: Facebook
Atiku ya ce wannan nadama da dawowa daga kuskure alama ce ta cewa akwai buƙatar gyara domin samar da jin daɗi ga kowa da kowa a ƙasar nan.
Atiku Abubakar ya bayyana cewa zaben 2027 ba zai kasance kamar yadda aka saba ba, domin yanzu akwai haɗin gwiwa da shirye-shirye masu ƙarfi daga ɓangarori daban-daban.
Atiku da Kwankwaso sun hadu a Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa manyan 'yan siyasar Najeriya da suka hada da Atiku Abubakar da Rabiu Musa Kwankwaso sun hadu a Abuja.

Kara karanta wannan
Sule Lamido ya tayar da kura bayan zargin Tinubu da mahaifiyarsa da rusa zaben Abiola
Manyan Najeriya sun taru a Abuja ne domin taya tsohon gwamnan Bauchi, Ahmadu Adamu Mua'azu murnar cika shekara 70.
An hango Atiku Abubakar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na musafaha suna dariya a yayin da taron ke tsaka da gudanawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
