"Abin da Ya Sa Muke Shirin Ƙirƙiro Jam'iyyar ADA kafin 2027," El Rufai Ya Yi Bayani
- Malam Nasir El-Rufai ya yi ƙarin haske kan dalili da ya sa haɗakar adawa ta zaɓi kafa sabuwar jam'iyyar siyasa kafin zaɓen 2027
- Tsohon gwamnan ya ce sun duba zaɓin kafa sabuwar jam'iyya domin kaucewa sharrin APC da ke haddasa rigingimu tsakanin ƴan adawa
- Tun farko dai jagororin adawa sun tura bukatar rijistar jam'iyyar ADA ga hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta watau INEC
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana abin da suka hanga wanda ya sa suka fara yunkurin ƙirkiro sabuwar jam'iyyar siyasa a Najeriya.
El-Rufai ya ce haɗakar adawa da ke shirin ƙwace mulki daga hannun APC a 2027, sun yanke kafa jam'iyya ne saboda gujewa cin amana da rikicin cikin gida da jam'iyyun adawa ke fama da su.

Kara karanta wannan
ADA: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da sabuwar jam'iyyarsu Atiku da El Rufai

Source: Twitter
Tsohon gwamnan ya yi wannan bayani ne da yake jawabi a cikin shirin Prime Time na kafar watsa labarai ta Arise News a daren Litinin.
Meyasa ƴan adawa suke shirin ƙirƙiro ADA?
A cewarsa, sun ɗauki matakin rijistar sabuwar jam'iyya mai suna ADA domin kaucewa ƙulli da munafurcin da gwamnatin APC ke shiryawa na raba kan ƴan adawa.
Ya ce haɗakar, wacce ta kunshi manyan jiga-jigan siyasa, ta duba hanyoyi biyu, na farko duba yiwuwar aiki da tsofaffin jam'iyyun adawa da kuma neman yi wa sabuwar jam'iyya rijista.
Malam Nasir El-Rufai ya ce:
"Ba a tafiya yaki da dabara ɗaya tal. Tun da muka fara tattaunawa, muka yanke cewa ba za su dogara da tsofaffin jam'iyyu ba, za mu duba yiwuwar kafa aabuwar jam'iyya.
Abin da ya sa haɗakar Atiku ta nemi rijistar ADA
Ya ce mafi yawan ƴan hadaƙar sun fi gamsuwa da kafa sabuwar jam'iyya, saboda za a samu sauƙin rigingimun cikin gida.
"Galibin jagororin da muke tare da su, sun fi yarda da a lalubo sabuwar jam'iyya saboda za ta zama da ƙarancin haɗari. Babu rikici da cututtukan cikin gida wanda APC da gwamnati mai ci ke haddasa wa."
El-Rufai ya kawo misalai daga cikin rigingimu da suka addabi jam’iyyun LP, PDP, da NNPP, yana zargin gwamnatin Tinubu da hannu don kassara jam'iyyun adawa.

Source: Facebook
El-Rufai ya zargi APC da haɗa faɗa a jam'iyyu
"Wadannan hanyoyi da jam’iyya mai mulki ke amfani da su abin kunya ne da rashin ɗa'a. Za su yi komai domin kawar da kowace jam’iyyar adawa."
“Shi ya sa shugabanni da dama suka ce hanya mafi aminci ita ce a kafa sabuwar jam’iyya tun da wuri," in ji shi.
El-Rufai ya kuma nuna shakku game da niyyar INEC na rajistar sabuwar jam’iyyar ADA, yana mai cewa yanayin siyasa a yanzu ya sauya ba kamar lokacin da suka kafa APC ba, rahoton Leadership.
Abubuwa 5 game da sabuwar jam'iyyar ADA
A wani labarin, kun ji cewa haɗakar shugabannin adawa karƙashin Atiku Abubakar ta miƙa bukatar rijistar sabuwar jam'iyya ADA ga INEC.
Jagororin wannan sabuwar jam’iyyar na cike da kwarin gwiwa cewa hukumar INEC za ta amince da bukatarsu kamar yadda doka ta tanada.
Legit.ng ta haskaka muhimman abubuwa biyar masu ban sha’awa game da jam'iyyar ADA da ake so a yi wa rajista.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

