Suswam: Tsohon Gwamna Ya Lissafo Mutum 2 da Suka Jawo Rikicin PDP

Suswam: Tsohon Gwamna Ya Lissafo Mutum 2 da Suka Jawo Rikicin PDP

  • Tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam ya yi magana kan rikicin da ya dabibaye jam'iyyar PDP tun 2023
  • Gabriel Suswam ya bayyana cewa Bala Mohammed da Umar Damagum su ne babbar matsalar jam'iyyar PDP
  • Tsohon gwamnan ya nuna cewa rashin yin abin da ya dace daga wajen waɗannan mutanen biyu, shi ne ya jawo PDP ta tsinci kanta a halin da take ciki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - An bayyana shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, a matsayin babbar matsala da ke damun PDP.

Wata babbar matsalar jam'iyyar kuma ita ce shugaban rikon ƙwarya na PDP, Ambasada Umar Damagum.

Gabriel Suswam
Gabriel Suswam ya tabo batun rikicin PDP Hoto: Gabriel Suswam
Source: Twitter

Tsohon gwamnan jihar Benue, Sanata Gabriel Suswam, shi ne ya bayyana hakan a wani shiri na tashar Arise Tv.

Wanene ake da zargi da laifi a rikicin PDP

Kara karanta wannan

Sule Lamido ya hango wanda zai zama shugaban ƙasa idan PDP ta rushe kafin 2027

Gabriel Suswan ya ce bai kamata a ɗora lwa Nyesom Wike laifi kan abubuwan da yake yi wa jam’iyyar PDP ba, ganin cewa waɗannan shugabanni sun ƙulla yarjejeniya da shi.

“Damagum shi ne babbar matsalar da muke da ita a jam’iyya. Bala Mohammed, a matsayinsa na shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP, shi ne ke jagorantarsa."
“Ba ya yin aikinsa yadda ya kamata. Kuma shi ya sa muke cikin wannan hali. Domin a yanzu, idan aka zo batun PDP, Bala shi ne kamar shugaban ƙasa, domin gwamnoni su ne ke ɗaukar nauyin tafiyar da jam’iyyar a yanzu."
“Suna bayar da kuɗi don gudanar da harkokin jam’iyya. Kuma Bala shi ne shugaban wannan ƙungiya, don haka shi ne shugaban jam’iyyar a halin yanzu. Idan bai jagoranci kwamitin gudanarwa na ƙasa yadda ya kamata ba, to laifin yana kansa."

- Gabriel Suswam

Ya ce gazawar shugabannin jam’iyyar wajen bin yarjejeniyar da suka ƙulla bayan ganawa da Nyesom Wike sau biyu a Lagos da Abuja, ya nuna rashin niyya mai kyau.

Gabriel Suswam ya nuna yatsa ga shugabannin PDP

Gabriel Suswam ya nuna cewa abin takaici ne yadda waɗannan shugabanni suka amince da wata yarjejeniya da suka san sauran masu ruwa da tsaki ba za su amince da ita ba, inda ya ce alama ce ta rashin amana.

Kara karanta wannan

Hasashen El Rufai ya tabbata, SDP mai kokarin kwace mulki ta shiga Matsala

Gabriel Suswam
Suswam ya nuna yatsa ga Damagum, Bala kan rikicin PDP Hoto: Gabriel Suswam
Source: Facebook
“Su ne manyan matsalolin da muke da su a PDP. Wannan zalunci ne. Idan da Bala da Damagum sun yi abin da ya kamata, da ba za mu shiga wannan kangin rikici ba a cikin jam’iyyar."

- Gabriel Suswam

A cewarsa, yayin da ake ƙoƙarin ceto jam’iyyar PDP da gaggawa, bai dace waɗannan shugabanni su ci gaba da zama matsala ga jam’iyyar ba.

“Idan ba mu da shugabanci nagari, to jam'iyya za ta ruguje. Abin da ya faru da PDP, a zahiri, shi ne rashin shugabanci da rashin ƙwarewar jagoranci a cikin jam’iyyar."

- Gabriel Suswam

Moro ya magantu kan rikicin PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa Abba Moro wakiltar Benue ta Kudu ya yi magana kan rikicin jam'iyyar PDP.

Sanata Abba Moro ya bayyana PDP ba za ta ruguje ba duk da rikicin cikin gida da ta tsinci kanta a ciki.

Hakazalika ya nuna ƙwarin gwiwarsa kan cewa Najeriya ba za ta taɓa zama ƙarƙashin jam'iyya ɗaya ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng