Rikici Ya Barke a PDP, An Dakatar da Tsohon Gwamna da Wasu Shugabanni Saboda Rashin Biyayya

Rikici Ya Barke a PDP, An Dakatar da Tsohon Gwamna da Wasu Shugabanni Saboda Rashin Biyayya

  • Rikicin jami'yya na kara ƙamari a jihar Benue inda PDP ke cigaba da daukan mataki kan shugabanninta saboda laifuffuka
  • A sabon rikici da ya barke, jami'yyar ta dakatar da wasu masu fada aji ciki har da Sanata Gabriel Suswan da Tergu Tsegba da sauransu
  • Kakakin jam'iyyar a jihar ya bayyana laifin da mutanen suka aikata da matakin da suka dauka kafin yanke hukuncin dakatar da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benue - Rikici a jam'iyyar PDP na kara ƙamari a jihar Benue da ke Arewa ta tsakiyan Najeriya.

Rahotanni na nuni da cewa jam'iyyar ta dakatar da wasu manyan ƴaƴanta saboda laifuffukan da suka aikata.

Kara karanta wannan

Bayan zanga zanga, Abba ya dauko muhimman ayyuka 7 domin farfaɗo da Kano

Jihar Benue
Rikicin jam'iyya ya kunno kai a PDP a jihar Benue. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa kakakin PDP, Bemgba Lortyom ya fadi dalilin dakatar da su daga jami'yyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabannin PDP da aka dakatar a Benuwai

Kakakin PDP a Benue ya bayyana cewa an dakatar shugabannin kananan hukumomin Apa, Gboko, Gwer-East Katsina-Ala, Konhisha, Logo, Otukpo da Ukum.

Haka zalika ya tabbatar da cewa cikin wadanda aka dakatar akwai Sanata Gabriel Suswam da Tergu Tsegba da Richard Gbande wanda manya ne a jam'iyyar.

Dalilin dakatar da shugabannin jam'iyyar PDP

Rahoton the Cable ya nuna cewa kakakin jam'iyyar ya bayyana cewa an samu mutanen da laifin nuna kin goyon bayan jam'iyyar da kuma rashin ladabi.

Ya bayyana cewa hakan na zuwa ne bayan an samu wasu yan daba sun kai hari sakatariyar jam'iyar da ke Makurdi tare da goyon bayan wasu ya'yan jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamnatin Abba Gida Gida ta amince da fitar da N2.67bn domin manyan ayyuka

Matakin da PDP ta dauka a farko

Kakakin jami'yyar, Bemgba Lortyom ya ce biyo bayan laifin an bukacesu su gurfana a gaban kwamitin ladabtarwa amma suka ƙi.

Biyo bayan haka ne kakakin ya ce jam'iyyar ta yanke hukuncin dakatar da su na wata daya daga tafiyarta a jihar Benue.

PDP da dakatar da Samuel Ortom

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta dauki muhimmin mataki bayan ta dakatar da tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom.

PDP ta dauki matakin dakatar da tsohon gwamnan ne kan zargin cin dunduniyarta musamman a tarurrukan jam'iyyar hamayyar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng