2027: Musulman Arewa Sun Bukaci Tinubu Ya Ajiye Shettima, Ya Dauki Kirista
- Wata ƙungiyar Musulmai a Arewa ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya zaɓi Kirista daga Arewa a matsayin mataimakinsa a 2027
- Ƙungiyar ta ce shawararta ta samo asali ne daga tattaunawa da dama da ta yi da shugabannin addini da kungiyoyin Musulunci a Arewa
- Ta bayyana cewa tikitin Musulmi da Musulmi ya samu nasara a 2023 saboda haɗin kan Kiristoci, don haka lokaci ya yi da za a saka musu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Wata ƙungiya mai rajin kare muradun Musulmai daga Arewa ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya zabi Kirista daga Arewa a matsayin abokin takararsa a zaɓen 2027.
Ƙungiyar ta bayyana wannan buƙatar ne a wani taron manema labarai da ta gudanar a ranar Lahadi.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa kungiyar ta bayyana cewa ta tattauna da kungiyoyin addini a Arewa kafin yanke wannan matsaya.
A cewar jagoran ƙungiyar, Bala Duguri, shawarar na da nufin ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya, tare da ƙarfafa nasarar shugaba Bola Tinubu a wa’adi na biyu.
Dalilin neman Bola Tinubu ya dauki Kirista
Bala Duguri ya bayyana cewa akwai bukatar yin adalci a harkar siyasa, musamman ganin yadda Kiristoci suka goyi bayan tikitin Musulmi da Musulmi a zaɓen 2023.
Shugaban kungiyar ya ce:
“A lokacin zaɓen da ya gabata, Kiristoci sun yi hadin kai don samar da nasara a Najeriya.
"Ya kamata a saka musu da alheri ta hanyar barin Kirista daga Arewa ya kasance mataimaki a 2027.”
An ba Shettima da Musulmai hakuri kan 2027
Ƙungiyar ta bukaci duk wani Musulmi mai muradin zama mataimakin shugaban kasa a 2027 da ya janye burinsa don bayar da dama ga Kirista.

Kara karanta wannan
2027: An samu wanda zai buga da Tinubu, jigo zai fito takarar shugaban ƙasa a APC
Duguri ya bayyana hakan ne da nufin tabbatar da cewa Najeriya ta samu ci gaba da dorewar zaman lafiya da hadin kai, wanda a cewarsa shi ne ginshiƙin kowace ƙasa mai son cigaba.

Source: Twitter
An bukaci APC ta duba yiwuwar daukan Kirista
Pulse Nigeria ta wallafa cewa kungiyar ta bukaci Shugaba Tinubu, shugabannin jam’iyyar APC da sauran masu ruwa da tsaki da su duba shawarar.
Duguri ya ce shawararsu ba ta da wata manufa ta siyasa, sai dai tana nufin ceto ƙasa daga rashin daidaito da kuma ƙarfafa nasarar shugaba Bola Tinubu.
Baya ga haka, Duguri ya ce za su cigaba da tattaunawa da sauran kungiyoyin musulmi a Arewa domin samar da mafita a 2027.
Musulmai sun yi wa Tinubu addu'a a Madina
A wani rahoton, kun ji cewa wasu malaman addinin Musulunci sun yi wa Bola Tinubu da Najeriya addu'o'i a kasa mai tsarki.
An gudanar da addu'o'in ne a wani zama da aka yi a birnin Madina yayin da mahajjatan Najeriya ke cigaba da isa Saudiyya domin aikin Hajjin bana.
Wani malamai da ya halarci taron addu'ar ya ce shugaba Bola Tinubu ya yi ayyukan alheri tun hawan shi mulki kuma saboda haka ne suka masa addu'ar.
Asali: Legit.ng
