Rigima Sabuwa: Kungiyoyi 56 Sun Nemi Akpabio Ya Yi Murabus kan Magudin Zabe

Rigima Sabuwa: Kungiyoyi 56 Sun Nemi Akpabio Ya Yi Murabus kan Magudin Zabe

  • Kungiyoyi fararen hula 56 sun bukaci shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da ya yi murabus bayan hukuncin kotu kan magudin zabe
  • Sun bayyana cewa hukuncin kotun daukaka kara ya tabbatar da cewa akwai magudi cikin sakamakon zaben da ya bai wa Akpabio nasara a 2019
  • Kungiyoyin sun ce ya wajaba ga Godswill Akpabio ya sauka daga kujerarsa a majalisa domin kare amincewa da tsarin dimokuradiyya a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Wasu fitattun kungiyoyin fararen hula 56 ciki har da Amnesty International Nigeria da CDD sun bukaci shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio da ya yi murabus.

Sun yi kiran ne a wata sanarwa da suka fitar bayan kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa Farfesa Peter Ogban.

Kara karanta wannan

Bashin Naira tiriliyan 4: Gwamnatin Najeriya ta fara hararo karin kudin wuta

Akpabio
An nemi Akpabio ya yi murabus kan magudin zabe. Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Farfesa Peter Ogban ne jami’in da ya bayyana sakamakon zaben majalisar dattawa na Akwa Ibom ta Arewa-Maso-Yamma a 2019.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun tabbatar da cewa an samu Farfesa Ogban da laifin canza sakamakon zabe domin bai wa Akpabio nasara.

Baya ga haka, an yanke masa hukuncin dauri na shekara uku da tarar N100,000 a 2021, kuma kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin a baya-bayan nan.

Kungiyoyi sun nemi Akpabio ya yi murabus

Kungiyoyin sun bayyana cewa hukuncin kotun ya jefa tambayoyi masu nauyi kan ingancin nasarar da Akpabio ya samu da kuma amincewar jama’a da tsarin dimokuradiyya.

A cewar sanarwar:

“Yanzu kotu ta tabbatar cewa an yi magudi domin bai wa Sanata Akpabio nasara.
"Ko da yake ya musanta hannu kai tsaye a cikin laifin, kasancewarsa wanda ya ci gajiyar magudin, ba ya iya kubuta daga zargi.”

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya fadi sirrin kawo karshen zubar da jini a Kaduna

Sun kara da cewa matsayin shugaban majalisar dattawa yana da muhimmanci ga kasa, don haka, a bisa tsarin gaskiya da amana, ya kamata Akpabio ya sauka domin a binciki lamarin a fili.

Kungiyoyi sun ce Akpabio ba zai kubuta ba

Kungiyoyin sun ce kasancewar Akpabio ya amfana da magudin zabe a 2019, ya kamata a sake nazarin cancantarsa ta tsayawa takara a 2023, balle har ya shugabanci majalisar dattawa.

Punch sun wallafa cewa kungiyoyin sun ce:

“Wannan batu ba siyasa ba ne, magana ce ta gaskiya da ladabtar da shugabanni.
"Najeriya na bukatar shugabannin majalisa masu kwarjini da tsafta a hukumance da kuma a ɗabi’ance.”

Kungiyoyin da suke nemi murabus din Akpabio

Baya ga Amnesty da CDD, wasu kungiyoyi da suka rattaba hannu a sanarwar sun hada da BudgIT, CJID, CISLAC, EiE Nigeria, HEDA, da Transition Monitoring Group (TMG).

Sauran sun hada da AFRICMIL, CLEEN Foundation, RULAAC, Accountability Lab Nigeria, Dataphyte, PWAN, Yiaga Africa, WARDC da Nigerian Feminist Forum (NFF).

Natasha Akpoti ta yi wa Akpabio shagube

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Natasha Akpoti da ke bugawa da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ta masa shagube.

Kara karanta wannan

Musa Kwankwaso ya faɗi maƙarƙashiyar da ake shiryawa NAHCON, Sheikh Pakistan

Sanata Natasha Akpoti ta yi wa Godswill Akpabio shagube ne a cikin wata wasika da ta rubuta masa.

Sanatar ta rubuta wasikar ne bayan an matsa lamba a kan cewa ya kamata ta ba Akpabio hakuri amma sai ta yi rubutu mai nuna wulakanci maimakon afuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng