"Ka Hakura da Shugaban Kasa": An Fadawa Atiku abin da Ya Kamata Ya Yi a 2027

"Ka Hakura da Shugaban Kasa": An Fadawa Atiku abin da Ya Kamata Ya Yi a 2027

  • Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya bukaci Atiku Abubakar da ya hakura da takarar shugaban kasa, ya ba matasa dama su jagoranci Najeriya
  • Tsohon hadimin shugaban kasar, ya gargadi Bola Tinubu da kada ya nemi tazarce a 2027, yana mai bayyana masu dalilai na rashin dacewar hakan
  • Hakeem Baba-Ahmed ya ce ya kamata ‘yan takarar da suka tsufa su yi murabus daga siyasa, ko kuma ‘yan Najeriya su yi masu ritayar dole

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon mai magana da yawun kungiyar dattawan Arewa, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya bukaci Atiku Abubakar da ya hakura da burin zama shugaban kasa.

A kwanan nan ne Dr Baba-Ahmed ya ajiye mukaminsa na matsayin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa a ofishin mataimakin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Rivers: An 'kunyata' matar shugaba Tinubu yayin gagarumin taro, mata sun yi bore

Baba-Ahmed ya shawarci Atiku da ya hakura da takarar shugaban kasa a zaben 2027
Atiku Abubakar | Hakeem Baba-Ahmed. Hoto: Atiku Abubakar, Hakeem Baba-Ahmed
Source: Facebook

Shawarar da Hakeem Baba-Ahmed ya fara ba Tinubu

Dr. Baba-Ahmed ya ce ya kamata Atiku, wanda ya tsaya takara har sau shida, ya cire burin zama shugaban kasa, ya ba matasa dama, a cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba a manta ba, a wata wasika da ya rubuta wa Bola Tinubu a ranar 23 ga Afrilu, Baba-Ahmed ya shawarci shugaban kasar da kada ya nemi tazarce a 2027.

Dattjiron na Arewa ya gargadi Tinubu cewa neman tazarce zai kasance babban kuskure a gare shi la'akari da yanayin tattalin arziki da siyasar kasar a halin yanzu.

Ya bukaci shugaban kasar da ya bai wa sababbin jini a siyasance dama, wadanda za su zo da sababbin dabaru da karsashi don ciyar da kasa gaba.

An nemi Atiku ya hakura da takara a 2027

Lokacin da aka tambaye shi a wata hira da aka yi da shi a Channels TV a ranar Alhamis ko zai bai wa Atiku irin wannan shawara, Baba-Ahmed ya ce zai ba shi shawara ya zama dattijon kwarai.

Kara karanta wannan

Hakeem Baba Ahmed ya fadi abin da ya sani kan alakar Tinubu da Shettima a Villa

“Idan na samu damar yin magana da Atiku, zan ce masa ya hakura. Ya yi iya kokarinsa. Ya kamata yanzu ya koma matsayin uba, da zai tallafa wa sababbin jini a shugabanci."

- Hakeem Baba-Ahmed.

Baba-Ahmed ya ce jam’iyyar adawa ta PDP na da damar samun nasara a zaben 2027 idan ta tsayar da matashi a matsayin dan takararta.

Ya kara da cewa

“In har suka tsayar da mai jini a jika, kuma matashi mai hangen nesa, suna iya doke APC. Najeriya na neman shugabanni masu hangen nesa da tausayawa jama'a.”

Ya jaddada cewa bai kamata a rika duba yanki ko kabila ba wajen zaben shugabanni a Najeriya, inda ya ce cancanta ya kamata ta zama ma'aunin zabe.

“Bai kamata mu cigaba da magana kan zaben dan Arewa ko dan Kudu ba. Abin da ake bukata shi ne mutumin da ya cancanta, kuma mai hangen nesa.”

- Hakeem Baba-Ahmed.

Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya shawarci su Atiku su hakura da takara, su barwa matasa
Dr. Hakeem Baba-Ahmed, tsohon hadimin Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Hakeem Baba-Ahmed
Source: Twitter

"Ku yi ritaya daga siyasa" - Baba-Ahmed ga su Atiku

Tsohon hadimin shugaban kasar ya ce ya kamata dattawan 'yan siyasa ire-irensu Atiku, Tinubu, Kwankwaso su yi murabus daga siyasa, ko kuma a tilasta musu yin hakan.

Kara karanta wannan

A ƙarshe, Hakeem Baba Ahmed ya fadi gaskiyar dalilin murabus a gwamnatin Tinubu

Da aka tambaye shi ko Atiku na PDP ko kuma Peter Obi na jam'iyyar LP za su iya tabuka abin kirki fiye da Tinubu da su ne suka samu mulki, Baba Ahmed ya ce:

“Gaskiya ban sani ba. Shi Peter Obi dai na san shi, farin sani, yana da kyawawan manufofi a wasu fannoni na shugabanci."

Game da Atiku kuwa, Hakeem Baba Ahmed ya ce duk da kwarewarsa, ba ya tunanin zai iyan fin Tinubu kyautatawa 'yan Najeriya.

“Abin da ya fi dacewa da wadannan 'yan takarar da suka manyanta shi ne su yi murabus da kansu. Idan ba su yi ba, to ‘yan Najeriya za su yi masu ritayar dole."

- Hakeem Baba-Ahmed.

Atiku ya yi tsufa ya yi takara?

A wata tattaunawa ta musamman da Legit Hausa, Suraj Caps ya yi martani kan masu cewa Atiku Abubakar ya hakura da takara saboda ya tsufa, yana mai cewa:

"Shi wannan zance da ake yi 'yanci ne, kowane dan kasa na da 'yancin fadin haka. Amma mu siyasa muke yi, kuma siyasa tana bukatar lissafi.
"Idan ka kalli gwamnatin shi Asiwaju da take ci yanzu, sannan ka dauko sauran 'yan takara, ka ce su sauya gwamnatin mai ci, to gaskiyar zance in ba Atiku Abubakar ba, ban yi tsammanin akwai wanda zai iya wannan ba."

Kara karanta wannan

'Dole Tinubu ya zarce,' Minista ya bukaci 'yan APC su tashi tsaye kan 2027

Matashin dan jam'iyyar ta PDP ya yi ikirarin cewa akwai shugabannin kasashe na duniya da sun girmi Atiku Abubakar, kuma hakan bai hana a zabe su ba.

"Yanzu idan ka kalli Donald Trump a Amurka, tsoho ne kuma ya girmi Atiku. Mu bukatarmu ba yaro ko tsoho ba, damuwarmu wanda zai kawo mana mafita a yanayin da muke ciki."

-Surajo Caps

Dalilin Baba-Ahmed na ajiye aiki a Aso Villa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya ce ya ajiye mukaminsa na mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan siyasa ne saboda rashin gamsuwa da tafiyar gwamnati.

A cewarsa, babu wani tabbataccen alamu da ke nuna cewa gwamnatin Tinubu na kokarin warware manyan matsalolin da suka dabaibaye ƙasar, musamman wadanda ta gada.

Ya bukaci Shugaba Tinubu da sauran fitattun 'yan siyasa su janye daga takarar 2027, su bar matasa su zo da sabbin tsare-tsare da hangen nesa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com