"Abin da Zai Rusa Hadakar da Atiku ke Jagoranta": Hadimin Wike

"Abin da Zai Rusa Hadakar da Atiku ke Jagoranta": Hadimin Wike

  • Hadimin ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya hango matsalar da za ta auku a shirin haɗakar manyan ƴan adawa
  • Lere Olayinka ya bayyana cewa tsakanin Peter Obi da Atiku Abubakar babu wanda zai yarda ɗaya ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa
  • Ya nuna cewa tuni haɗakar ta mutu murus tun kafin tafiya ta yi nisa saboda an ƙafa ta ne don cimma muradin Atiku na yin takara

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Lere Olayinka hadimin ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan haɗakar da Atiku Abubakar ke jagoranta.

Hadimin na Wike ya bayyana cewa haɗakar da Atiku Abubakar ke jagoranta ta mutu murus tun kafin ta fara ƙarfi.

Atiku Abubakar, Peter Obi
Hadimin Wike ya ce hadakar Atiku ta mutu Hoto: Atiku Abubakar, Peter Obi
Source: Twitter

Lere Olayinka ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar Arise TV a ranar Alhamis, 1 ga watan Mayun 2025.

Kara karanta wannan

"Ɗan Arewa kaɗai," Dele Momodu ya faɗi wanda zai iya kayar da Shugaba Tinubu a 2027

Olayinka ya ce haɗakar ba za ta yi aiki ba domin Peter Obi ba zai yarda da wani tsarin siyasa da za a kitsa don goyon bayan burin Atiku na tsayawa takarar shugaban ƙasa ba.

Atiku da Peter Obi sun yi aiki tare

Idan ba a manta ba a shekarar 2019, Atiku da Obi sun tsaya takara tare a matsayin ɗan takarar shugaban kasa da mataimakinsa karkashin jam’iyyar PDP.

Shekara hudu bayan haka, kowannensu ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyya daban, bayan da Obi ya fice daga PDP zuwa jam’iyyar LP kafin zaɓen 2023.

Yanzu da zaben 2027 ke kara matsowa, Atiku, wanda ke kiran a kafa hadaka domin kwace mulki daga hannun Tinubu, ya gayyaci Obi da wasu fitattun ƴan adawa da su hada kai da shi a wannan yunƙuri.

Meyasa haɗakar ba za ta yi tasiri ba?

Sai dai Olayinka ya dage cewa manufar kafa wannan haɗaka ita ce domin cika muradin Atiku na zama shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Okowa ya bayyana lokacin da Atiku zai fice daga jam'iyyar PDP

"Da zaran ana maganar haɗaka, kuma haɗakar na da nufin cika burin mutum ɗaya, wane ne ke magana kan hadaka? Alhaji Atiku Abubakar. Wane ne ke son cin moriyar hadakar? Alhaji Atiku Abubakar."
"Ta yaya to haɗakar za ta yi aiki? Idan aka kafa hadaka don amfanar Alhaji Atiku Abubakar, haɗakar ba za ta yi aiki ba."

- Lere Olayinka

Nyesom Wike
Hadimin Wike ya ce hadaka ta mutu Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Source: Facebook

Hadimin Wike ya hango saɓani tsakanin Atiku, Obi

Olayinka ya ƙara da cewa haɗakar ba za ta yi aiki ba saboda Atiku da Peter Obi ba za su iya cimma matsaya kan wanda ya kamata ya tsaya takara a ƙarƙashin haɗakar ba.

“Shin akwai wani abu da ke tafiya daidai a cikin wannan haɗakar yanzu? Ta mutu tun kafin a fara ta. Za su ce Atiku zai tsaya tare da Peter Obi."
"Shin Peter Obi zai yarda ya tsaya tare da Atiku Abubakar? Shin Atiku zai yarda Peter Obi ya tsaya takarar shugaban ƙasa karkashin haɗakar?"
"Ko Peter Obi zai yarda wani daban ya tsaya takara? Wadannan su ne matsalolin. Ba za ta yi aiki ba, kuma ba za ta taɓa yin aiki ba."

Kara karanta wannan

Bayan komawa APC, Okowa ya fadi nadamarsa kan takara da Atiku a 2023

- Lere Olayinka

Atiku ya magantu kan ficewa PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya yi magana kan batun zai fice daga jam'iyyar PDP.

Atiku ya bayyana cewa bai da wani shiri na ficewa daga jam'iyyar inda ya ba da tabbacin ci gaba da kasancewarsa a PDP.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya nuna cewa bai san daga inda masu yaɗa cewa zai bar PDP suke samo bayanansu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng