Sanata Ya Dorawa Atiku Laifi kan Rikicin PDP, Ya Fadi Kuskuren da Ya Yi

Sanata Ya Dorawa Atiku Laifi kan Rikicin PDP, Ya Fadi Kuskuren da Ya Yi

  • Sanata mai wakiltar Benue ta Kudu, Abba Moro, ya koka kan rikicin da ya addabi jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya
  • Abba Moro ya bayyana cewa Atiku Abubakar ya gaza wajen warware rikicin da ya mamaye jam'iyyar PDP mai hamayya
  • Sanatan ya nuna cewa ya kamata Atiku ya ɗauki matsayin jagora wajen haɗa kan PDP bayan rashin nasarar da ta yi a 2023

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa, Abba Moro, ya nuna yatsa ga Alhaji Atiku Abubakar kan rikicin da ya addabi jam'iyyar PDP.

Sanata Abba Moro ya nuna kuskuren Atiku kan gazawa wajen taka rawa a matsayin jagora don warware rikicin da ke addabar PDP.

Abba Moro ya caccaki Atiku Abubakar
Sanata Abba Moro ya ce ya gaza wajen warware rikicin PDP Hoto: Atiku Abubakar, Comrade Abba Moro
Source: Facebook

Yayin wata hira da tashar Channels Tv a ranar Talata, Sanata Abba Moro ya bayyana cewa Atiku ya kasa haɗa kan jam’iyyar PDP bayan zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

An gano kuskuren da ya jawo Atiku Abubakar ya fadi zaben 2023 a PDP

Sanatan mai wakiltar Benue ta Kudu, ya danganta rikicin PDP da rashin jagoranci daga Atiku bayan rashin nasarar jam’iyyar a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Jam'iyyar PDP na fama da rikicin gida

Jam’iyyar PDP ta fada cikin rikici tun bayan faduwar da ta yi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, rikicin da ya kara tsananta kwanan nan bayan ficewar manyan jiga-jigai daga jihar Delta, ciki har da Gwamna Sheriff Oborevwori zuwa APC.

Sauya sheƙa daga PDP a jihar Delta ya girgiza shugabancin jam’iyyar, kasancewar jihar na ɗaya daga cikin inda take da ƙarfi tun daga shekarar 1999.

Yayin da rikicin jam’iyyar ke ci gaba ba tare da mafita ba, ana kuma raɗe-raɗin cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a 2023, Alhaji Atiku Abubakar, na tunanin ficewa daga PDP ƙafin zaɓen 2027.

Me Sanata Moro ya ce kan Atiku?

Da aka tambaye shi wanda ya kamata ya ja ragamar fitar da PDP daga wannan rikici, Sanata Moro ya ce ya Atiku ne ya kamata ya ɗauki nauyin warware matsalar jam’iyyar, duba da burinsa na sake neman kujerar shugaban ƙasa ƙarƙashin PDP.

Kara karanta wannan

Bayan kalaman Okowa, Atiku ya yi magana kan ficewa daga PDP

Sanata Abba Moro
Sanata Abba Moro ya yi magana kan rikicin PDP Hoto: Comrade Abba Moro
Source: Twitter
"Duba da burinsa na takara a wancan lokaci da kuma fatan sake takara, na yi tsammanin Alhaji Atiku Abubakar zai fara tun daga ranar farko bayan zaɓen 2023 da ƙoƙarin haɗa PDP da dawo da haɗin kai a cikin jam’iyyar."
“Don haka, a gaskiya, ina ganin idan akwai wani mutum a wancan lokaci da ya kamata ya haɗe jam’iyyar bayan mummunar faduwar da PDP ta yi a zaɓen 2023, wannan mutumin tabbas shi ne Alhaji Atiku Abubakar."

- Sanata Abba Moro

Atiku ya magantu kan ficewa daga PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yi magana kan ficewa daga jam'iyyar.

Wazirin Adamawa ya bayyana cewa bai da wani shiri na ficewa daga jam'iyyar PDP wacce ya yi takara a cikinta a shekarar 2023.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ce bai san inda masu yaɗa jita-jitar ficewarsa daga PDP suke samo bayanansu ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng