Atiku Abubakar Ya Yi Zazzafan Martani ga Tinubu kan Dakatar da Gwamna Fubara
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar ya soki Bola Ahmed Tinubu bisa ayyana dokar-ta-ɓaci a Ribas
- Atiku ya yi Allah wadai da wannan mataki wanda ya bayyana shi a matsayin farmaki ga tsarin demokuraɗiyya a Najeriya
- Wazirin Adamawa ya ce duk mai bibiyar abubuwan da ke faruwa tsakanin Fubara da tsagin Wike ya san akwai hannun Tinubu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi kakkausar suka ga matakin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka na ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas.
Atiku ya bayyana cewa matakin ba komai ba ne face siyasa kuma cike yake da gurɓatacciyar niyya da wata manufa ta siyasa.

Asali: Twitter
Wazirin Adamawa ya yi raddi kan dakatar da Gwamna Fubara ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a daren Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya zargi Tinubu da hannu a rikicin Ribas
Atiku ya bayyana cewa duk mai bibiyar rikicin siyasar Ribas zai fahimci cewa Tinubu yana da hannu kai tsaye a rikicin da ya addabi jihar.
Ya ce gazawa ce babba ga Tinubu da ya kasa shawo kan wannan rikici, kazalika naɗe hannun shugaban kasa da ƙin yin wani abu don warware matsalar abin kunya ne matuƙa.
"Ban da wannan batu na siyasa a Ribas, muna ganin yadda matsalar tsaro ta ta'azzara har ta kai ga rusa muhimman gine-ginen ƙasa a jihar.
"Wannan laifi ne da ke wuyan Shugaban Ƙasa, domin mulkinsa ne ya ba da damar faruwar hakan kuma ya kasa daƙile shi,"
- in ji Atiku Abubakar
Yankin Neja Delta ya koma gidan jiya
Ya ce rashin iya mulki da gazawar shugabancin Tinubu sun jefa yankin Neja Delta cikin mawuyacin hali, inda suka koma gidan jiya.
Atiku ya ce gazawar Tinubu ta maida Neja Delta zamanin tashin hankali da rikici, wanda ya rusa zaman lafiyar da marigayi Shugaba Umaru Musa Yar'Adua ya tabbatar.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce shekaru da dama na kwanciyar hankali sun salwanta saboda wasu munafukan dabaru da maguɗin siyasa.
Bugu da ƙari, Atiku ya bayyana cewa idan har an lalata kayan more rayuwa a Ribas, to shugaban ƙasa ne ya kamata ya ɗauki alhakin hakan.

Asali: Depositphotos
Atiku ya yi Allah-wadai da matakin
Ya ce rashin adalci ne hukunta mutanen Ribas kawai saboda rikicin siyasa da ke tsakanin gwamnan jihar da wasu jiga-jigan gwamnatin tarayya da ke goyon bayan Tinubu.
"Abin da ke faruwa a Ribas ba wai rikicin siyasa ba ne kawai, hari ne kan dimokuraɗiyya. Kuma dole ne a yi Allah-wadai da shi da kakkausar murya,"
- in ji Atiku.
A ƙarshe, ya buƙaci 'yan Najeriya su fito su ƙalubalanci irin wannan salo na siyasa, yana mai cewa dole ne a kare 'yancin mutane daga mummunan tasirin son zuciya da rigingimun siyasa.
Ribas: Tinubu ya naɗa gwamnatin riƙo
A wani labarin, an ji cewa Bola Tinubu ya naɗa tsohon hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas (mai ritaya) a matsayin wanda zai jagoranci al'amuran Ribas.
Tinubu ya ɗauki wannan mataki ne bayan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimkiyarsa na tsawon watanni shida, duk a kokarin shawo kan rikicin siyasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng