Wike Ya Kai 'Yan PDP Makura, An Fara Neman a Kore Shi daga Jam'iyya saboda Tinubu
- Kungiyar kwararru a jam'iyyar PDP ta bukaci a dauki matakin korar Ministan Abuja, Nyesom Wike daga jam’iyya
- Wannan ya biyo bayan karan tsaye da mara wa shugaba Bola Ahmed Tinubu baya da Wike ya ke yi duk da shi dan PDP ne
- Kungiyar ta yi barazanar maka Wike a gaban kotu saboda cin zarafin PDP da na 'ya'yan jam'iyyar da ake zarginsa da yi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Kungiyar kwararru a jam'iyyar adawa ta PDP, (CP-PDP) ta bukaci a kori Ministan Abuja, Nyesom Wike, bisa zargin cewa yana kokarin durkusar da jam’iyyar.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, kungiyar ta soki Wike bisa goyon bayan da ya bai wa shugaba Bola Ahmed Tinubu domin sake tsayawa takara a 2027.

Kara karanta wannan
An sake rikita Tinubu, Kwankwaso, Obi da gwamnonin PDP sun shirya raba shi da mulki

Asali: Facebook
Daily Trust ta ruwaito cewa a wani taro da aka yi kwanan nan, Wike ya yi alkawarin mara wa Tinubu baya, tare da sukar Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) na PDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP ta zargi Nyesom Wike da rashin biyayya
Trust radio ta wallafa cewa ungiyar CP-PDP ta zargi Wike da rashin biyayya, tana mai cewa ya koma goyon bayan APC, karara ba tare da la'akari da cewa shi dan PDP ba ne.
Saboda haka, sun bukaci Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) na PDP da ya dauki matakin korarsa daga jam’iyya.

Asali: Facebook
Kungiyar ta gargadi cewa:
"Idan PDP na son cigaba da rayuwa, akwai iyaka ga irin wannan hali. Siyasa ta na da nasaba da muradi. Mutane ba su kamata su yi amfani da wasu su watsar da su ba."
Shugaban kungiyar, Barrister Obinna Nwachukwu, ya ce:
"Wike ya ketare iyaka. Yana bata sunan jam’iyya tare da cin mutuncin shugabanninta."
"Za mu kai Wike kotu," 'Yan PDP
'Ya 'yan na PDP sun kuma yi barazanar hana Wike halartar duk wani taron jam’iyyar, tare da shigar da kara a kotu bisa zargin bata sunan PDP.
Sun ce:
"Lauyoyinmu na tattara hujjoji don gabatar da kara a kotu. Wike ya daina kai hari ga PDP ko kuma ya fuskanci hukunci."
Jam'iyyar PDP ta gaji da halin Wike
Mataimakin Sakataren Yada Labarai na PDP, Ibrahim Abdullahi, ya shaida wa Legit cewa jam’iyyar ta gaji da shari’o’in da tsohon gwamnan Ribas, Nyesom Wike ya shigar kotu don hana PDP korarsa.
Ya ce wannan yunkuri na Wike na kokarin haddasa rudani a jam’iyyar ba zai yi nasara ba, kuma wannan ba ya nufin ya fi karfin jam'iyya.
A cewarsa:
"Wadannan umarnin kotu sun fara yin yawa, amma PDP koyaushe tana shawo kan irin wadannan matsaloli. Mun tsira daga rikice-rikicen siyasa da dama, kuma wannan ma ba zai wuce ba."
Wike ya gargadi gwamnan PDP
A wani labarin, kun ji cewa Ministan Babban Birnin Tarayya kuma tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya gargadi gwamna Siminalayi Fubara tare da yi masa barazana.
Ya bayyana cewa yanzu gwamnan ya fara fuskantar matsaloli a siyasa, kuma abin da ke gaba ya fi wanda ya gani tsanani duba da yunkurin tsige shi da majalisar Ribas ke kokarin yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng