'Ya Na da Bakin Jini': An Fadi Kuskuren El Rufai da Yake Alakanta Kansa da Buhari

'Ya Na da Bakin Jini': An Fadi Kuskuren El Rufai da Yake Alakanta Kansa da Buhari

  • Hadimin Atiku Abubakar, Abdul Rasheeth, ya bayyana cewa yankin Arewa ba ya da sha’awar duk abin da ya shafi Muhammadu Buhari yanzu
  • Rasheeth ya mayar da martani ne bayan Buhari ya sake jaddada biyayyarsa ga jam’iyyar APC bayan Nasir El-Rufai ya koma jam'iyyar SDP
  • El-Rufai ya ce ya sanar da Buhari kafin ya bar APC zuwa SDP, wannan ya sa tsohon shugaban kasar ya nesanta kansa da watsi da jam'iyya
  • A cewar Rasheeth, danganta kansa da Buhari yanzu kawai zai kara dagula lamarin tsohon gwamnan na Kaduna ne a idon 'yan Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Hadimin Atiku Abubakar ya ce yankin Arewa bai sha’awar wani abu da ya shafi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Abdul Rasheeth ya fadi haka ne yayin da yake martani ga kalaman Mai girma Muhammadu Buhari kan cewa ya na nan daram a jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Sanata ya watsawa matasa kasa a ido, ya ki amincewa ya kara da Tinubu a 2027

Hadimin Atiku ya fadi kuskuren El-Rufai na alakanta kansa da Buhari
Hadimin Atiku Abubakar ya ce Nasir El-Rufai ya jefa kansa a matsala kan tarayya da Buhari. Hoto: @elrufai, @atiku.
Asali: Twitter

Buhari ya jaddada biyayyarsa ga jam'iyyar APC

Rasheeth ya fadi hakan ne yayin da yada wani rubutu a shafinsa na X, yayin da yake mayar da martani kan wata sanarwar da Buhari ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar, tsohon shugaban kasar ya sake jaddada goyon bayansa ga jam’iyyar APC da yake cikinta tun kafuwarta.

Sanarwar Buhari ta fito ne bayan hirar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi inda ya ce ya sanar da Buhari kafin sauya sheka.

A cikin sanarwar, Buhari ya ce ba zai taba mantawa da halaccin da APC ta yi masa ba kuma har yanzu cikakken 'danta ne.

El-Rufai ya bayyana cewa ya samu amincewar Buhari kafin ya bar APC zuwa jam’iyyar SDP, domin ci gaba da fafutukar siyasa.

Kalaman El-Rufai game da tattaunawarsa da Buhari ya jawo maganganu inda wasu ke zargin dattajon da cin dunduniyar APC yayin da wasu ke cewa ba shi da wani tasiri a Arewa a yanzu kam.

Kara karanta wannan

'Ku biyo ni TikTok': El-Rufai ya bude shafinsa, ya tara dubban mabiya cikin sa'o'i 24

An ba El-Rufai shawara kan alaka da Buhari
Hadimin Atiku Abubakar ya ce kuskure ne El-Rufai ke yi wurin alakanta kansa da Buhari. Hoto: Atiku Abubakar.
Asali: Facebook

Kuskure El-Rufai wurin alakanta kansa da Buhari

Rasheeth ya ce danganta kansa da Buhari kan batun sauya sheka zai kara jefa El-Rufai cikin matsaloli a yankin Arewa.

Ya ce:

"Da a ce za ka iya ganin yadda mutanen Arewa suka mayar da martani da yadda suka yi tsokaci a BBC Hausa."
"A cikin hirar, El-Rufai ya ce ya shaida wa Buhari cewa zai bar APC, wannan ya jawo masa karin matsala kawai."
"A lokacin da Arewa ke kin jin duk wani abu da ya shafi Buhari, ya yi kuskure wajen alakanta kansa da tsohon shugaban kasar."

Seyi Tinubu ya gana da Buhari a Kaduna

A wani labarin, kun ji cewa dan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu, da Ministan Matasa, Ayodele Olawande, sun kai ziyara ta musamman gidan tsohon shugaban ƙasa.

Malam Bashir Ahmad, tsohon hadimin Buhari, ya tabbatar da ziyarar a daren ranar Talata, 4 ga watan Maris, 2025, ta shafinsa na X inda ya yada hotunan haduwar ta su.

Kara karanta wannan

Bayan kalaman El-Rufai game da komawa SDP, Buhari ya fadi matsayarsa a APC

Wannan na zuwa ne yayin da Seyi Tinubu ke ci gaba da yawatawa yankin Arewacin Najeriya inda yake rarraba abinci yayin da ake azumin Ramadan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng