Wasu Mawakan Kannywood Sun Watse Wa Kwankwasiyya, Sun Kama Layin Barau a APC
- Mawakan Kannywood, Adamu Hassan Nagudu da Yusuf Karkasara sun sauya sheka daga NNPP zuwa jam’iyyar APC mai mulki
- Mawakan sun bayyana ficewarsu daga Kwankwasiyya yayin wata ziyarar da suka kai wa Sanata Barau Jibrin a birnin Abuja
- Bayan sauya shekar, sun kafa kungiyoyi biyu masu suna 'Naka Sai Naka' da 'Barau Mafita' domin tallata ayyukan jam’iyyar APC
- Wasu kungiyoyi biyu na matasa da Fulani, 'Tafiya Daya' da 'Fulbe Kano Barau Mafita', suma sun shiga hadin gwiwa da mawakan a taron
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Fitattun mawakan Kannywood biyu, Adamu Hassan Nagudu da Yusuf Karkasara, sun sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.
Mawakan, Nagudu da Karkasara sun bayyana ficewarsu daga jam’iyyar NNPP da tafiyar Kwankwasiyya a ziyarar da suka kai wa Sanata Barau Jibrin.

Kara karanta wannan
Manyan ƴan siyasa, jam'iyya da El-Rufai ya ziyarta kafin yanke shawarar barin APC

Source: Facebook
Mawakan Kannywood sun watsar da Kwankwasiyya
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin shi ya tabbatar da haka a shafinsa na Facebook a yau Laraba 12 ga watan Maris, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mawakan Kwankwasiyyar sun hada kai da wasu a Kannywood domin kafa kungiyoyin 'Naka Sai Naka' da 'Barau Mafita'.
Kungiyoyin na da burin tallata ayyukan jam’iyyar APC tare da nuna goyon baya ga shugabannin jam’iyyar a matakin kasa da jihohi.
Haka kuma, wasu kungiyoyi biyu, 'Tafiya Daya' karkashin Mustapha Rabiu da 'Fulbe Kano Barau Mafita' sun halarci taron da mawakan.

Source: Facebook
Alkawuran da kungiyoyi suka yi wa Barau Jibrin
Kungiyar 'Fulbe Kano Barau Mafita' na Fulani ne da ke da burin tallata manyan ayyukan da jam’iyyar APC ke yi a jihar Kano.
Barau ya ce:
"Na tarbi sababbin ‘yan jam’iyyar tare da mika musu gaisuwa, na kuma taya su murna bisa daukar wannan matsayar da ta dace.
"Na bayyana cewa sun zabi jam’iyya mafi kyau a nahiyar Afirka, jam’iyyar da ke tsaye kan dimokradiyya da ‘yancin jama’a.
"Ina bukatar kungiyoyin ukun ku hada kai da aiki tare domin samun nasarar jam’iyyarmu ta APC a gaba.
"Ina jaddada muhimmancin matasa a al’umma, duba da yadda suke da rinjaye cikin yawan jama’ar kasar nan."
Sanata Barau ya ce matasa na bukatar jagoranci da horo mai kyau domin tabbatar da makoma mafi inganci ga Najeriya da ci gabanta.
Ya kuma yi alkawarin ba su dukkan goyon baya da suke bukata domin tabbatar da nasarar APC a jihar da Najeriya baki daya.
Barau Jibrin ya sake kassara tafiyar Kwankwasiyya
Mun ba ku labarin cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi wasu jiga-jigan kungiyar malaman Kwankwasiyya guda 23 zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Barau ya karbi 'yan uwan Gwamnan Kano, ciki har da Mahbub Nuhu Wali, wadanda suka bar jam'iyyar NNPP inda suka shiga APC tare da jefar da jajayen huluna.
Bayan ganawa da su a Majalisa, tawagar ta raka shi 'A-Class Event Centre', a nan ne suka tarbi magoya bayan Atiku Abubakar daga jihohi 19 na Arewacin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
