'Ku Tsige Shi': Minista Ya Bukaci Majalisa Su Tuge Yaronsa daga Kujerar Gwamna
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce idan Simi Fubara ya aikata laifi, majalisa ta tsige shi, domin ba laifi ba ne a siyasa
- Wike ya nuna damuwa da yadda wasu 'yan majalisa uku ke ƙoƙarin kafa doka, yana mai sukar matakin zuwa kotun koli
- Ya ce Gwamna Fubara ya raina dattawan da suka taimaka masa, kuma ya na zargin abokan aikinsa da cin moriyar jihar
- Wike ya kalubalanci PANDEF, yana mai cewa ƙungiyar na hana kokarin sasancin Bola Tinubu da kuma ɓata siyasar yankin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya yi magana kan rigimar siyasa da dambarwa da ke faruwa a jihar Rivers.
Nyesom Wike ya ce ya kamata a tsige Gwamna Siminalayi Fubara idan ya aikata abin da ya cancanta a raba shi da kujerar.

Source: Facebook
Wike ya zargi Fubara da cin amana
Wike ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa kai tsaye da manema labarai, ya nuna damuwarsa kan rikicin siyasa da ke faruwa a jihar Rivers, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan ya koka kan yadda rikicin ya ki karewa inda yake zargin wasu da ci gaba da ruruta rigimar domin biyan buƙatar kansu.
Wike ya tuna yadda dattijo Ferdinand Alabararba ya yi ƙoƙarin ganin dan Ijaw ya zama gwamna, amma daga baya aka ci mutuncinsa.
Ya kare kansa cewa yana mutunta doka da oda, yana mamakin yadda 'yan majalisa kaɗan ke ƙirƙirar doka da kuma neman hukuncin kotu.
Wike ya ce:
“Wannan dattijo har da kuka, wannan yaron daga baya ya zazzage shi, yanzu ba zai iya komawa ya nemi taimakonsa ba.
“Ina mamakin yadda a kasar nan, mutane uku za su kafa doka, su kuma je kotun koli."

Source: Facebook
Wike ya fadi yadda ake tafiyar da siyasa
Wike ya yaba wa masu kalubalantar abin da bai dace ba, yana mai jaddada cewa ‘yan majalisa ba bayi ba ne, an zaɓe su ne kamar kowa, cewar Channels TV.
Wike ya kara da cewa:
“Shugabannin majalisa ba yaranmu ba ne, an zaɓe su, na yi tafiya da su, na gina alaƙa da su, ba a matsayin maigida da yaransa ba ne.
"Siyasa ba wasa ba ce. Idan ya aikata abin da ya dace a tsige shi, su tsige shi, tsigewa ba laifi ba ne,”
Wike ya zargi abokan gwamna Fubara da amfani da shi da kuma cin moriyar jihar, yana sukar kungiyar PANDEF da kiranta ƙungiya mafi muni.
Wike ya tada ƙura da cewa ba kowane Ijaw ne ke da rinjaye ba a yankin Neja Delta, yanabayyana bambancin kabilar Kalabari da Opobo.
An hana gwamna Fubara shiga majalisa
Mun ba ku labarin cewa Gwamna Fubara tare da tawagarsa sun isa Majalisar jihar Rivers a yau Laraba, 12 ga watan Maris, 2025 amma bisa mamaki suka tarar da ƙofofin a rufe.
Jami'an tsaron da ke gadin Majalisar sun bayyana cewa sun hana gwamnan shiga ne saboda bai turo sanarwar zuwansa a hukumance ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

