Manyan 'Yan Siyasar Arewa Sun Fara Lallaba Jonathan, Ana Son Ya Nemi Kujerar Tinubu
- Wasu manyan ‘yan siyasa daga Arewa sun fara tuntubar tsohon shugaban ƙasa, Dr. Goodluck Jonathan domin ya tsaya takara a zaɓen 2027
- Matakin na zuwa a lokacin da 'yan adawa su ka bayyana cewa ana samar da hadaka na kawancen 'yan adawa don raba Tinubu da kujerarsa
- Rahotanni na nuna cewa wasu ‘yan siyasa daga Arewa ba su gamsu da yadda ake tafiyar da mulkin ƙasar nan ba, musamman a fannin tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Northern Nigeria — Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ba zai nemi tsayawa takarar shugaban kasa a PDP ba idan Goodluck Jonathan ya tsaya takara
Shugabannin siyasa a Arewa da ba su gamsu da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ba suna aiki a asirce domin tsayar da dan takarar su a zaben 2027.

Asali: Facebook
Thisday ta wallafa cewa gwamna Bala Mohammed, ya ce ba zai nemi tikitin jam’iyyar PDP ba idan aka shawo kan tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan siyasar Arewa sun yi watsi da Tinubu
Jaridar Legit ta wallafa cewa shugabannin siyasar Arewa, wadanda ke wakiltar kuri'u mafi yawa da ake kadawa a Najeriya, sun nuna rashin amincewa da shugaba Bola Tinubu.
Rahotanni sun ce suna kokarin jawo tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan domin ya tsaya takara a 2027 don karawa da Tinubu a zaben.
Wasu majiyoyi da ke da masaniya kan shirin sun ce kalaman da Gwamna Bala Mohammed ya yi kwanan nan na cewa ba zai nemi takara ba idan Jonathan ya tsaya ba wai zato ba ne kawai.
Dalilin 'yan Arewa na watsi da Tinubu
Kiran da ake yi wa Jonathan ya karbi tikitin takara ya karu bayan zanga-zangar #EndBadGovernance da aka yi a fadin kasar
Wannan, ta zama wata manuniya a kan yadda mazauna Arewacin kasar nan su ka nuna rashin gamsuwa da salon mulkin shugaba mai ci.
An gudanar da zanga zangar ne saboda tsadar rayuwa, yunwa, karancin kudi a hannun jama'a, matsalar tsaro da sauran batutuwa da su ka addabi jama'a.
Tinubu: Martanin tsagin Jonathan ga Arewa
Duk da kokarin shugabannin siyasar Arewa, an gano cewa har yanzu Jonathan bai nuna sha’awar tsayawa takara ba.

Asali: Facebook
Wasu daga cikin na kusa da shi sun bayyana cewa yana mayar da hankali kan ayyukan kasa da kasa da kuma agaji, ba siyasa ba.
Guda daga cikin makusantansa da aka sakaya sunansa, ya kara da cewa Goodluck Jonathan ya ce tattaunawa kan zaben 2027 da wuri.
Zaben 2027: Ana yunkurin kayar da Bola Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa tsohon sakataren yaɗa labaran PDP, Kola Ologbondiyan, ya ce ana shirin kafa ƙawance tsakanin jam’iyyun adawa domin kalubalantar jam’iyya mai mulki, APC.
Ologbondiyan ya ce shirin da ake yi ba ƙarami ba ne, domin ana haɗa ƙarfi da ƙarfe domin kifar da APC daga mulki a babban zaɓen 2027, inda ya ce manyan 'yan siyasa za su hadu guri guda.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng