Nasir El Rufa'i Ya Sauya Sheka, Ya Fita daga APC zuwa SDP

Nasir El Rufa'i Ya Sauya Sheka, Ya Fita daga APC zuwa SDP

  • Nasir El-Rufai ya fice daga jam’iyyar APC, ya koma SDP bisa dalilai da ya ce na rashin daidaito a tafiyar siyasarsa
  • Wata wasika da ke yawo a kafafen sada zumunta ta nuna tsohon gwamnan ya mika takardar murabus dinsa daga APC a mazabarsa
  • Hakan na zuwa ne bayan El-Rufai ya gana da manyan jiga-jigan 'yan adawa, ciki har da Atiku Abubakar da Rauf Aregbesola

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya fice daga jam’iyyar APC, ya zabi jam’iyyar SDP a matsayin sabon dandalin siyasarsa.

Wata wasika da ke yawo a kafafen sada zumunta ta nuna cewa El-Rufai ya mika takardar murabus dinsa ga jam’iyyar APC a mazabarsa da ke garin Kaduna.

Kara karanta wannan

Ana zargin El Rufai zai fice daga APC, ɗansa Bashir ya nuna jam'iyyar da ya koma

El'Rufa
Ana rade-radin El-Rufa'i ya koma SDP. Hoto: Nasir El-Rufa'i
Asali: Facebook

Legit ta gano haka ne a cikin wani sako da tsohon gwamnan ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta wallafa cewa tsohon gwamnan ya bayyana rashin gamsuwa da tafiyar jam’iyyar APC a wasikar da ya rubuta.

Dalilin ficewar El-Rufa'i daga APC

A cikin wasikar da ya rubuta, El-Rufai ya bayyana cewa ya sadaukar da kansa don gina APC tun daga hadewar jam’iyyun siyasa a shekarar 2013.

Sai dai ya ce abubuwan da suka faru cikin shekaru biyu da suka gabata sun nuna cewa jam’iyyar APC ba ta da sha’awar yin gyara ko inganta tafiyar ta.

A cewarsa, ya sha yin kokarin fadakarwa a sirrance da kuma a fili kan matsalolin jam’iyyar, amma ba a dauki matakin da ya dace ba.

Yadda magoya bayan El-Rufai suka karbi labarin

Wani hadimin El-Rufai da ya taba zama kwamishina a gwamnatinsa ya bayyana cewa ficewar El-Rufai daga APC abu ne da aka dade ana jira.

Kara karanta wannan

Rikici ya ƙara Kamari, jam'iyyar APC ta buƙaci gwamna ya yi murabus cikin sa'o'i 48

Majiyar ta ce El-Rufai ya yi shawarwari da manyan abokansa na siyasa kafin yanke hukuncin sauya shekar.

EL-Rufa'i
El-Rufa'i ya gana da Atiku. Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Twitter

Magoya bayansa sun ce ba su yi mamakin bullar wasikar ba, domin dama sun san yana dab da barin APC saboda rashin jituwa da shugabancin jam’iyyar.

Tattaunawa da jiga-jigan adawa

A makonnin da suka gabata, El-Rufai ya gana da manyan ‘yan adawa, ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da kuma tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola.

Bugu da kari, El-Rufai ya gudanar da tarurruka da shugabannin SDP domin tsara yadda tafiyarsa za ta kasance a cikin jam’iyyar.

A Jihar Kaduna, an ruwaito cewa daya daga cikin magoya bayansa, Nasiru Abdullahi Maikano, ya zama sabon shugaban rikon kwarya na jam’iyyar SDP.

Haka zalika na dan El-Rufa'i mai suna Bashir ya daura alamar jam'iyyar SDP a wani sako da ya wallafa a X a yau Litinin.

Kara karanta wannan

'PDP za ta dawo mulki a 2027,' Martanin jama'a kan ziyarar El Rufa'i ga Atiku

APC ta fara kamfen kan tazarcen Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta fara yakin neman zabe ta bayan fage ga shugaba Bola Tinubu a wasu yankunan Arewa.

Shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje da wasu manyan jam'iyyar sun yi magana kan tazarcen Tinubu a wurare da dama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel