Gwamnan PDP Ya Shawo kan Kusoshin Jiharsa, Sun Bar Atiku Sun Koma Layin Tinubu

Gwamnan PDP Ya Shawo kan Kusoshin Jiharsa, Sun Bar Atiku Sun Koma Layin Tinubu

  • Gwamna Siminalayi Fubara ya shawo kan jagororin Ribas, sun juyawa Atiku Abubakar baya sun koma layin shugaba Bola Tinubu
  • Chief Abiye Sekibo, tsohon ministan sufuri, ya bayyana hakan yayin da ya shaidawa Tinubu cewa mutanen Ribas na tare da shi
  • Ya bayyana cewa Fubara ya kawo ci gaba a Ribas duk da ƙalubalen tattali, inda ya nemi Tinubu ya kyale masu kushe gwamnan a wajensa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ribas - Tsohon ministan sufuri, Chief Abiye Sekibo, ya bayyana yadda shi da wasu jagororin jihar Ribas suka juyawa Atiku Abubakar baya suka koma layin shugaba Bola Tinubu.

Chief Abiye Sekibo, ya ce gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya shawo kan kusoshin jihar suka koma goyon bayan Tinubu.

Tsohon minista yayi magana kan kokarin da Fubara ke yi na ci gaban gwamnatin Tinubu
Tsohon minista ya bayyana yadda Fubara ya shawo kansu suka koma layin Tinubu. Hoto: @SimFubaraKSC, @officialABAT, @atiku
Asali: Twitter

Yadda kusoshin Ribas suka bar Atiku zuwa Tinubu

Kara karanta wannan

Ramadan: An fadi dalilin faduwar farashin abinci karon farko cikin shekaru 10 a azumi

Tsohon ministan ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da sabunta ofishin kashe gobara na Borokiri da Gwamna Fubara ya gudanar a Fatakwal, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Chief Abiye ya ce Fubara ne ya shawo kansu suka sauya sheka daga tafiyar Atiku zuwa tafiyar Tinubu, yana mai jaddada goyon bayansu ga shugaban kasa a yanzu.

Babban kusa a jihar ta Ribas, ya rok sShugaba Tinubu da kada ya saurari masu cewa Gwamna Fubara na yin abubuwan da suke adawa da gwamnatinsa.

"Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, muna tare da kai. A koyaushe mutanen Ribas suna marawa gwamnatin tarayya baya,"

- inji Chief Abiye.

Tsohon minista ya aika sako ga Tinubu

Chief Abiye ya shaidawa Tinubu cewa Gwamna Fubara ya nuna wa mutanen Ribas cewa dole ne su tsaya tsayin daka tare da shugaban kasa.

Tsohon ministan ya ce wasu na kokarin yada jita-jita cewa Atiku ne ke da rinjaye a cikin gwamnatin Fubara, amma hakan ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

Ana zargin an lakadawa hadimin tsohon gwamna duka kan sukar sanatan Jigawa

Punch ta ruwaito Chief Abiye yana cewa:

"Ko a Abuja akwai magoya bayan Atiku. Amma gwamna Fubara ya shawo kanmu cewa abun da ya fi dacewa shi ne mu tsaya bayan shugaban kasa.
"Akwai wasu da za su rika fada maka maganganu daban daban, musamman a kan mutane irina, wadanda 'yan a mutun Atiku ne, mun san za a ce maka ai yaran Atiku ne ke tare da gwamna.
"Ya shugaban kasa, ka sani a yanzu goyon bayanmu yana tare da shugaban kasarmu, kuma muna tare da kai. Muna tare da kai saboda hakan ne ya dace."

Ya kara da cewa Bola Ahmed Tinubu ne halastaccen shugaban da aka zaba a zaben 2023, don haka dole su mara masa baya.

Tsohon minista ya jinjinawa Gwamna Fubara

Tsohon minista a Ribas lokacin bude ginin gashe gobara da Fubara ya sabunta
Gwamna Fubara tare da Chief Abiye a wajen bude ginin kashe gobara a Ribas. Hoto: @SimFubaraKSC
Asali: Twitter

Tsohon ministan ya kuma kara da cewa, bayan shekaru 24, al’ummar Ijaw sun samu damar yin gwamna daga yankinsu a Ribas, don haka dole ne su tsaya bayan Fubara.

Kara karanta wannan

Obasanjo @ 88: Tinubu ya jinjina, ya jero alheran tsohon shugaban Najeriya

"Zaben da aka yi ne ya ba danmu damar zama gwamna, a karon farko cikin shekaru 24 al'ummar Ijaw sun samu damar yin gwamna. Muna tare da shi, ba mu da zabi."

- Chief Abiye.

Ya ce Fubara ya nuna kwarewa da kishin kasa, ta hanyar tabbatar da ci gaban jihar da hadin kan Najeriya gaba daya.

Tsohon ministan ya ce duk da kalubalen tattalin arziki da ake fuska, hakan bai hana Fubara ya tabbatar da cewa babu matsala a jihar Ribas.

Tinubu ya shiga ganawa da Gwamna Fubara

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya gana da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas da shugabannin Ogoniland a Aso Villa, Abuja.

An rahoto cewa Gwamna Fubara ya isa fadar shugaban ƙasa domin taron tare da Sanata Lee Maeba da wasu wakilan yankin Ogoniland.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng