'Adawa Ta Kare': Tsofaffin Masu Sukar Tinubu 8 da Yanzu Suka Zama Makusantansa
- An bayyana gwagwarmayar siyasar Shugaba Bola Tinubu a matsayin abin da nazari ga duk wani matashi mai sha'awar siyasa
- An ce Tinubu ya tara makiya da masoya, kuma an samu masoyansa da suka koma makiyansa a hanyarsa ta zama shugaban kasa
- Sai dai a wannan karon, Legit Hausa ta tattaro bayanin wasu manyan masu adawa da Tinubu da yanzu suka zama makusantansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Gwagwarmayar siyasar Shugaba Bola Tinubu ta kasance za ta iya zama babban darasi da matasa masu burin shiga siyasa za su so karantawa.
Duniya ta shaida cewa Tinubu ya tara abokanai da makiya da dama. Ya yi abokanai da suka zama makiya, haka kuma makiya da suka zama abokanai.
Kafin ya ci zabe, Tinubu ya fi samun makiya, musamman saboda tikitin Muslim-Muslim da ya yi tare da Kashim Shettima, mataimakin shugaban kasa na yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da haka, wasu daga cikin wadanda ake kira makiyan wannan tikiti a yanzu sun koma makusantan shugaban kasa Tinubu a cewar rahoton ThisDay.
Ga jerin wasu daga cikin makiyan da suka zama abokansa:
1. Daniel Bwala
Daniel Bwala, ya kasance tsohon kakakin kungiyar yakin neman zaben Alhaji Atiku Abubakar, wanda ya yi takara da Tinubu a zaben shugaban kasa na 2023.
An nada Bwala a matsayin mashawarci na musamman kan harkokin watsa labarai da sadarwa na shugaban kasa, duk da tarihin sukar Tinubu da ya yi a baya.
Kafin nadin nasa, Bwala ya dade da nuna tsantsar adawa da halayya da cancantar Tinubu (wani lokaci a cikin kakkausar suka) a madadin tsohon mataimakin shugaban kasar.
Nadin Bwala ya jawowa Tinubu suka, inda Jesutega Onokpasa, wani jigon APC, ya ce shugaban ya ci amanar wadanda suka taimaka ya ci zabe, inji rahoton Arise News.
2. Festus Keyamo
Mista Festus Keyamo, SAN, wanda ya kasance babban dan adawar jam’iyyar APC, ya samu tukuicin mukamin minista har sau biyu bayan sauya sheka.
Keyamo, a wata hira da yayi da Mujallar Time a shekarar 2000, ya bayyana cewa Bola Tinubu ya lalata ilimi a Legas, ya saye ra'ayin gidajen jaridu, ya kuma ba majalisar jihar cin hanci.
Duk da wannan kazafi, sai ga shi Tinubu ya nada Festus Keyamo a matsayin kakakin yakin neman zabensa, lamarin da ya jawo mutane suka nuna mamakin wannan kawance.
A wani rahoton Vanguard, Reno Omokri ya taba zargin Keyamo da zama silar rashin kawo karsshen yajin aikin ASUU saboda tallata Tinubu da yake yi a 2022.
3. Bosun Tijani
Olatunbosun Tijani wanda aka haife shi a 1977 ya kasance ɗan kasuwa kuma wanda ya zama ministan sadarwa, kirƙira da tattalin arziki na zamani, tun daga 2023, inji rahoton WikiPedia.
Tijjani, tsohon jagoran muryar kungiyar Obidients a kafofin sada zumunta, ya zama minista duk da zarge-zargen kalaman batanci da ya yi wa Tinubu a baya.
Punch ta rahoto cewa a lokacin tantancewarsa a majalisar dattawa, Tijani ya amince cewa ya yi wasu rubuce-rubuce na fusata a baya amma ya nemi afuwar 'yan majalisar.
Nadin Tijjani mukamin minista ya kara fito da tsarin siyasar Shugaba Bola Tinubu na cewa siyasa ba ta da makiyi ko masoyin dindindin.
4. Femi Pedro
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Legas, Femi Pedro ya shiga cikin kwamitin yakin neman zaben Shugaba Bola Tinubu tare da wasu masu sukarsa na baya.
A lokacin da Tinubu ya na gwamnan Legas, an ce an kitsa tsige Pedro daga mukamin mataimakin gwamnan jihar Legas kan zarge-zargen rashin da’a.
An ce tun daga lokacin, Fedro ya kullaci Tinubu tare da ci gaba da sukar gwamnatinsa saboda yana tunanin kamar da hannunsa a cire shi daga mataimakin gwamna.
A 2013, alamun sulhu sun bayyana a fili tsakanin Tinubu da Pedro. Rahoton WikiPedia ya nuna cewa sarkin Legas ya karfafa sulhun bayan Tinubu ya halarci bikin auren dan Pedro a 2012.
A Disambar 2013, Pedro ya yi wata ganawar sirri da Tinubu, gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi da shugaban riko na APC na kasa, Cif Bisi Akande, domin kammala komawarsa APC.
5. Musiliu Obanikoro
Musiliu Obanikoro ya kasance tsohon minista kuma jakada, wanda ya hakura da adawa da Tinubu tare da komawa mai biyayya a gare shi.
Obanikoro ya taba zama minista a karkashin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kuma ya jaraba yin takarar gwamnan Legas a karkashin PDP.
Jaridar Premium Times ta rahoto rahoto cewa an tafka musayar baki tsakanin Tinubu da Obanikoro a 2014, inda har PDP ta sha alwashin kare muradun Obanikoro.
Bayan sasanta rikicinsa da Tinubu, Obanikoro na daya daga cikin wadanda suka kare tsare tsaren Tinubu kan tattalin arziki, kamar yadda rahoton ya nuna.
6. Femi Fani-Kayode (FFK)
Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama na daya daga cikin masu sukar Tinubu kafin ya sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki shekaru uku da suka wuce.
An nada Femi Fani-Kayode, darakta na karamin kwamitin yakin neman shugaban kasa na jam’iyyar APC a bangaren sababbin kafafen yada labarai.
Lokacin da ya aka fara sukarsa kan dawowa mai kare Tinubu, FFK ya ce yana tare da 'aladu' ne a lokacin amma ya gane gaskiya tare da komawa APC, inji rahoton Daily Trust.
A wata hira da Channles TV, Fani-Kayode, ya bayyana cewa ya koma kare Tinubu saboda wani dalili na kashin kasa da kuma hadin kan kasa.
7. Adeseye Ogunlewe
Tsohon sanata kuma dan takarar gwamna, Ogunlewe ya kasance daya daga cikin manyan masu adawa da Tinubu a siyasar Legas, amma yanzu ya koma gefensa.
A wata hira da Punch, tsohon sanatan ya bayyana ra’ayinsa na baya game da Tinubu, yana mai cewa lokaci ya canza kuma dole ne a yi nazari kan manufofin shugaban kasar.
An tambayi Ogunlewe ko har yanzu na kan bakansa na cewa Tinubu ba dan asalin Legas ba ne, ya amsa da cewa ya canja ra'ayi, kuma ya gano Tinubu na da wayau da basira.
Ogunlewe na daga cikin wadanda suka taimaka a yakin neman zaben Tinubu kuma har yanzu yana ci gaba da kare gwamnatin APC.
8. Olusegun Dada
Tsohon mai sukar Tinubu, Dada ya zama babban masoyinsa, wanda hakan ya sa aka nada shi a matsayin mataimaki na musamman kan harkokin sada zumunta.
Kafin nadin nasa, Dada ya kasance mai sukar Tinubu a kai a kai har zuwa lokacin da ya lashe tikitin takarar shugaban kasar Najeriya.
Ma'abota shafukan sada zumunta sun sha wallafa wasu daga cikin kalaman Olusegun Dada na batanci da ya yi a kan Tinubu, yayin da suke mamakin komawarsa yaron shugaban.
"Siyasa ba da gaba ba" - Hon. Idris
Hon. Idris Ibrahim, tsohon mai neman takarar dan majalisar Katsina na karamar hukumar Funtua, ya ce dama ita siyasa ana yinta ne ba da gaba ba.
Hon. Idris ya ce a siyasa ne za ka samu masu adawa da kai yau, gobe su rikide su koma masoyanka, don haka ita ba ta da masoyi ko makiyin dindindin.
Ga waɗanda suke ganin Tinubu na kuskuren nada tsofaffin 'yan adawarsa mukamai, Hon. Idris ya ce akwai hikimar siyasa a hakan.
"Ai idan ka ga makiyinka, kuma ka hango cewa yana da amfani, to janshi za ka yi a jiki, har ya koma masoyinka, domin ya yi maka wannan amfanin.
"Ita siyasa a duniya ake yinta, kuma kowa yana yinta ne domin riba. Yayin da ake siyasa domin kare muradun al'umma, dole ne a kare muradun rai."
- cewar Hon. Idris.
An titsiye mai sukar Muslim Muslim
A wani labarin mun ruwaito cewa an titsiye Daniel Bwala, mai sukar tikitin takarar Muslim Muslim kan shiga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
An tambayi Daniel Bwala dalilin karɓar matsayi a gwamnati duk da cewa har yanzu Tinubu da Kashim Shettima ba su canza addini ba, tambayar da ya gagara amsawa ba.
Asali: Legit.ng