2023: Magoya bayan Tinubu sun kaddamar da yakin neman zabe

2023: Magoya bayan Tinubu sun kaddamar da yakin neman zabe

- Manyan magoya bayan jagoran jam'iyyar APC na kasa, Ahmed Bola Tinubu, sun kaddamar da yankin neman zabensa a Ibadan

- Magoya bayan da suka hadi da tsaffin, ministoci, yan majalisa da jiga-jigan 'yan siyasa sun mika rokonsu ga Tinubu ya amsa kirarsu

- Yan kwamitin yakin neman zaben sun yi kira ga al'ummar yankin kudu maso yamma da sauran sassar Najeriya su mara wa Tinubu baya

Wasu magoya bayan jagoran jam'iyyar, APC, na kasa, Sanata Ahmed Bola Tinubu, a ranar Talata a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, sun kaddamar da yakin neman zaben shugabancin kasarsa kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Gabanin kaddamar da kwamitin kamfin din karkashin jagorancin tsohon Ministan Ayyuka, Adedayo Adeyeye daga Jihar Ekiti, kwamitin ta ziyarci Oba na Ibadan, Oba Saliu Adetunji da Alaafin na Oyo, Oba Lamidi domin neman addu'a.

2023: Magoya bayan Tinubu sun kaddamar da yakin neman zabe
2023: Magoya bayan Tinubu sun kaddamar da yakin neman zabe. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Jerin zuri'a 5 da suka fi arziki a Najeriya

Duk da cewa Tinubu bai riga ya sanar da niyyarsa ta fitowa takarar shugaban kasar ba, an dade ana yada jita-jitar cewa tsohon gwamnan na Jihar Legas na son tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

'Yan siyasa da mabiya jagoran na jam'iyyar APC na kasa da dama sun hallarci kamfen din da aka kaddamar a dakin taro na Muace 21.

Daga cikinsu akwai tsohon karamin Ministan Tsaro, Musliu Obanikoro; Shugaban kwamitin yakin neman zaben na SWAGA 2023, Sanata Dayo Adeyeye, Sanata Adesoji Akanbi, mai wakiltar Oyo ta Kudu da tsohon dan majalisar wakilai na tarayya, Otunba Abayomi Ogunnusi.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Wasu da ake zargi da fashi da garkuwa sun tsere daga gidan yari

Wasu daga cikin mahalarta taron sunyi jawabi daban daban na nuna muhimmancin shiga a dama da su domin zaben wanda zai shugabanci Najeriya daga shekarar 2023.

"Muna kira gare shi ya amsa kirar mu kuma muna kira ga dukkan al'ummar Kudu maso Yamma su mara masa baya don ya zama shugaban Najeriya. Ko wacce yanki a kudu tana da ikon fitar da takara amma wanda ya fi jajircewa ne zai yi nasara. Kada ku manta, dukkan 'yan Najeriya ne za suyi zaben," a cewar Adeyeye cikin jawabin da ya yi.

A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke shugaban hukumar daukan ma'aikata, Dakta Nasiru Mohammed Ladan Argungu daga mukaminsa.

Sanarwar saukewar na kunshe ne cikin wata wallafa da babban mataimakin shugaban kasa a bangaren watsa labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Sanarwar ta ce Buhari ya umurci karamin ministan Kwadago da Ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ya nada shugaban riko daga cikin manyan direktocin hukumar don maye gurbin Argungu a yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel