Peter Obi Ya Durkusa a Gaban Shugaba Tinubu? An Gano Gaskiya

Peter Obi Ya Durkusa a Gaban Shugaba Tinubu? An Gano Gaskiya

  • Wani fitaccen mai amfani da manhajar X ya yi iƙirarin cewa Peter Gregory Obi ya ɗurkusa a gaban Shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • A hoton da ya sanya a shafinsa na X ya nuna Rabiu Musa Kwankwaso tare da Shugaba Tinubu da Peter Obi
  • Wani dandali na binciken gaskiya ya binciki iƙirarin tare da bayyana sakamakonsa a cikin wani rahoto da aka fitar a ranar Laraba, 3 ga watan Afrilu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wani mai amfani da manhajar X ya yi iƙirarin cewa Peter Obi ya durƙusa a gaban shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Ayekooto (@DeeOneAyekooto), ya sanya hoton tare da taken, "Mutunta duk wanda yake gaba da kai."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi buda baki da jiga-jigan APC, ya fadi tanadin da ya yi wa 'yan Najeriya

Peter Obi da Shugaba Bola Tinubu
Peter Obi da Tinubu sun yi takara a zaben shugaban kasa na 2023 Hoto: Mr. Peter Obi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ayekooto wanda ɗan jam'iyyar APC ne yana da mabiya a shafinsa na X sama da 337,000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Peter Obi ya durƙusa a gaban Tinubu?

Hoton da ya sanya ya nuna Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, yana ɗurkusawa a gaban Shugaba Bola Tinubu.

Rabiu Kwankwanso ɗan takarar jam’iyyar New Nigerian People Party (NNPP) a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, shi ma ya fito a wannan hoton.

Duk da cewa Kwankwaso da Obi sun gana da niyyar haɗa kai don yaƙar jam’iyyar APC ta Tinubu a zaɓen 2023, ƙawancen na su bai yiwu ba.

Ya zuwa yammacin ranar Laraba, 3 ga watan Afirilun 2024, mutum 100 sun yi martani kan hoton, mutum 150 sun sake wallafa shi yayin da ya samu 'likes' sama da 1,000.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Wike ya bayyana abin da ya yi shirin yi da Atiku ya kayar da Tinubu

Menene gaskiya kan hoton?

Duba da yadda aka yi ta magana kan hoton a shafukan sada zumunta, dandalin binciken gaskiya na Dubawa, ya gudanar da bincike a kansa.

Bayan kammala bincike a kan hoton, Dubawa ya yanke hukunci a ranar Laraba, 3 ga watan Afirilu cewa an yi amfani da wata fasaha ne wajen sauya ainihin yadda hoton yake.

Dubawa ya bayyana cewa:

"Bincikenmu ya nuna cewa hoton da mai amfani da X ɗin ya sanya, wani hoto ne da aka ɗauka a ranar, 26 ga watan Afirilun 2023 wanda aka sauya. Saboda haka iƙirarin da ya yi ƙarya ce."

Dalilin Obi na buɗa baki da musulmai

A wani labarin kuma, kun ji cewa kakakin kungiyar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ta jam'iyyar Labour Party (LP), Yunusa Tanko, ya faɗi dalilin Peter Obi na yin buɗa baki tare da musulmai.

Tanko ya ce Obi ya saba da cudanya da jama'a shiyasa ya yo buɗa bakin saɓanin iƙirarin da ake yi cewa ya je saboda siyasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel