Yaron Tsohon Gwamna Ya Jagoranci Zanga Zanga, Ya Nemi Tinubu Ya Sauka Daga Mulki

Yaron Tsohon Gwamna Ya Jagoranci Zanga Zanga, Ya Nemi Tinubu Ya Sauka Daga Mulki

  • Jama’a sun shirya zanga-zanga a lokacin da gwamnatin Najeriya ta ke murnar zagayowar ranar tuna damukaradiyya
  • Kasim Balarabe Musa ya na ganin babu wani abin murna a ranar, ya jagoranci zanga-zangar lumuna a garin Kaduna
  • Yaron tsohon gwamnan na Kaduna ya bukaci Bola Tinubu ya magance matsalolin kasar ko dai ya bar kan karagar mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Kaduna - Kasim Balarabe Musa ya jagoranci wata zanga-zangar lumuna da aka shirya domin kokawa da halin da al’umma ke ciki.

An yi wannan zanga-zanga ne a ranar 12 ga watan Yuni yayin da ake bikin zagayowar ranar murnar dawowa mulkin damukaradiyya.

Bola Tinubu
Yaron tsohon Gwamnan Kaduna yana so Bola Tinubu ya gyara Najeriya Hoto: @Nosasemota
Asali: Twitter

Zanga-zanga kan mulkin Bola Tnubu

Kasim Balarabe Musa ya jagoranci wannan zanga-zangar lumuna ne a garin Kaduna kamar yadda Vanguard ta kawo labarin a makon nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban APC ya fallasa wanda ya jawo ake binciken gwamnatin El-Rufai

A wajen wannan zanga-zanga ne Kasim Balarabe Musa ya yi Allah-wadai da gwamnatin APC da ke mulki karkashin Bola Ahmed Tinubu.

Kasim Balarabe Musa yana cikin ‘ya ‘yan Balarabe Musa wanda ya yi mulki a jihar Kaduna.

Marigayi Balarabe Musa ya zama gwamna a karkashin jam’iyyar PRP mai adawa a 1979, daga baya rikicin siyasa ya jawo aka tsige shi.

Kasim: "Babu abin da Tinubu ya tsinana"

A cewar Kasim Balarabe Musa, tun da shugaban kasa Bola Tinubu ya shiga ofis a 2023, babu wani abin alfahari da za a nuna a mulkinsa.

Matashin ya fadawa ‘yan jam’iyyar PRP cewa Najeriya ta ci-baya a karkashin mulkin APC.

Kasim ya ce mahaifinsa da irinsu Cif Gani Fawehinmi SAN da Shehu Sani sun yi kokari wajen ganin an dawo mulkin farar hula a Najeriya.

A yau, yana ganin kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba ganin yadda ake fama da tsadar rayuwa a hannun wadanda suka canji sojojin.

Kara karanta wannan

Ana daf da zaɓe, ƙanin Gwamna ya watsa masa ƙasa a ido, ya bar jam'iyyar PDP

An fadawa shugaba Tinubu ya sauka

Punch ta rahoto shi yana cewa talakawa ba su iya cin abinci duk da arzikin kasar nan baya ga kashe-kashe da tabarbarewar al’amura.

Kasim Musa ya ba shugaba Bola Tinubu shawarar ya canza dabarunsa ta yadda za a iya magance matsalolin da suka addabi Najeriya.

Idan kuwa kalubalen sun fi karfin Tinubu, ya nemi shugaban kasar ya yi murabus domin wannan ne mafi munin lokaci tun 1960.

APC, Tinubu, Uba Sani da El-Rufai

A jihar ta Kaduna, an ji labari tsohon shugaba a jam’iyyar APC ya yi hasashen Bola Tinubu da Gwamna Uba Sani za su rasa tazarce a 2027.

Alhaji Salihu Muhammad Lukman ya ce wani babba a APC ya hada-kai da fadar shugaban kasa a yaki Mal. Nasir El-Rufai saboda siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel