Allah ya yi wa tsohon gwamnan Kaduna, Balarabe Musa rasuwa
- Tsohon gwmnan Kaduna, Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ya rasu
- Marigayin ya rasu ne a safiyar ranar Laraba a gidansa da ke Aliyu Turaki Road Unguwar Sarki Kaduna
- Ya rasu yana da shekaru 84 a duniya kuma za ayi jana'izarsa a yau Laraba
Rahotannin da muka samu ta tabbatar da rasuwar tsohon gwamnan Jihar Kaduna Abdulkadir Balarabe Musa.
'Yar marigayin ta tabbatar da cewa ya rasu a safiyar ranar Laraba a kamar yadda The Cable ta ruwaito.
A cewarta, za ayi masa jana'iza a yau da rana.
Tsohon sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani shima ya sanar da rasuwar tsohon gwamnan a shafinsa na Twitter a ranar Laraba 11 ga watan Nuwamba.
KU KARANTA: Wanda ya yi ƙarar Rahama Sadau ya ce fadar shugaban kasa da wani kwamishinan 'yan sanda ke hana a kama ta
A sakon da ya wallafa a Twitter, Shehu Sani ya rubuta "Alhaji Balarabe Musa ya rasu a yau. Allah ya jikan rai ya kuma saka masa da gidan Aljanna Firdausi. Amin."
DUBA WANNAN: Rahama Sadau ta yi magana kan rahotannin kama ta da gurfanar da ita a kotu
Balarabe Musa ne gwamna na farko da aka fara tsige wa a tarihin Najeriya.
Har wa yau, shine shugaban jam'iyyar People’s Redemption Party (PRP) a jamhuriyya ta hudu amma ya sauka daga mukamin a shekarar 2018 saboda ya kula da lafiyarsa.
A wani labarin, kungiyar kare hakkin musulmi (MURIC) ta bukaci a kama kuma a gurfanar da Rev. Fr. Godfrey Igwebuike Onah, wata huduba da ya yi a coci na tunzura matasan kiristoci a Nsukka, jihar Enugu, da su kai hari kan musulmai da kuma lalata masallatai a garin.
Shugaban MURIC, Ishaq Akintola, wanda ya yi wannan batun a ranar Juma'a a wata sanarwa, ya ce kungiyar ta goyi bayan Majalisar Ƙolin Harkokin Addinin Musulunci (NSCIA) a karar da ta shigarwa DSS na a kama tare da gurfanar da Rev. Onah.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng