Ana Daf da Zaɓe, Ƙanin Gwamna Ya Watsa Masa Ƙasa a Ido, Ya Bar Jam'iyyar PDP

Ana Daf da Zaɓe, Ƙanin Gwamna Ya Watsa Masa Ƙasa a Ido, Ya Bar Jam'iyyar PDP

  • Kanin Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya fice daga jam'iyyar PDP ana daf da gudanar da zaben gwamna a jihar
  • Benjamin Obaseki ya watsar da jam'iyyar kan rashin iya shugabanci bayan shafe shekaru ana damawa da shi
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake ta shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan jihar a watan Satumba mai zuwa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zabe, kanin Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya watsa masa kasa ido.

Jigon jami'yyar PDP, Benjamin Obaseki wanda ya kasance kanin gwamnan ne ya fice daga jam'iyyar ana daf da zaben gwamna.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamnan da aka tsige da ɗan majalisar tarayya sun koma bayan APC

Kanin gwamna Obaseki ya yi murabus daga PDP ana daf da zabe
Gwamna Godwin Obaseki na Edo ya samu matsala bayan kaninsa ya yi murabus daga PDP. Hoto: Godwin Obaseki.
Asali: Facebook

Edo: Jigon PDP ya yi murabus

Benjamin wanda ya yi kaurin suna a jam'iyyar ya kasance jigo kuma mai fada aji a karamar hukumar Oredo a cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan hadimin gwamnan na musamman, Clem Aziegbemi shi ma ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC.

Sanarwar barin PDP da Benjamin ya yi na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya mika ga shugaban jam'iyyar a karamar hukuma, PM News ta tattaro.

Musabbabin barin PDP da Benjamin ya yi

"Ina mai rubuta wannan takarda domin sanarwa a hukumance na yi murabus daga PDP da muka gina ta tare ta zama mafi girma a baya."
"Na yi nadamar barin jam'iyyar da muka gina ta tun daga tushe amma lokaci ya yi da ya kamata na gina kai na."

Kara karanta wannan

"Duk da masu ja da ikon Allah, mun yiwa mutanen Kano aiki," Gwamna Abba gida gida

"A yanzu, shugabannin jami'yyar sun rikice sun rasa inda za su shawo kan matsalolinta wanda yana daga cikin abin da ya fi damu na."

- Benjamin Obaseki

Benjamin ya ce ragamar jam'iyyar a hannun Gwamna Obaseki hatsari ne kuma babu alamun nasara a gaba.

An cafke jigon jam'iyyar PDP a Edo

Kun ji cewa, an kama mataimakin daraktan yada labarai na jam’iyyar PDP a yakin neman zaben gwamnan Edo, Rabaran Olu Martins.

Rundunar ‘yan sandan jihar ce ta kama Rabaran Martins kan zargin furta kalaman batanci da tunzura jama'a, kuma ta gurfanar da shi gaban kotu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.