Fetur Daga N200 Zuwa N800 da Yadda Abubuwa Suka Canza Daga Buhari Zuwa Tinubu

Fetur Daga N200 Zuwa N800 da Yadda Abubuwa Suka Canza Daga Buhari Zuwa Tinubu

Abuja - Shekara guda kenan da Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya gaji Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasar Najeriya.

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Rahoton Legit Hausa ya duba yadda farashin abubuwa da sauran alkaluma su ka canza bayan da Bola Tinubu ya karbi mulki.

Muhammadu Buhari da Bola Tinubu
Muhammadu Buhari da Bola Tinubu da ya gaje shi a Aso Villa Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Buhari zuwa Tinubu: Canjin abubuwa a kasuwa

1. Tinubu ya cire tallafin man fetur

A lokacin da Muhammadu Buhari ya bar ofis, ana saida litar fetur ne a kan kusan N230, yanzu farashin ya kai N700 zuwa N750.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Dizil ya tashi a gidajen mai

A gidajen mai dizil ya kai N844 a watan Mayun 2023, yanzu kowace lita ta doshi N1415 a karkashin jagorancin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Muhimman ayyuka 15 da Gwamnatin Abba tayi cikin shekara 1 a jihar Kano

3. Hauhawar farashin kayan masarufi

Alkaluma daga NBS sun tabbatar da cewa an samu tashin farashin kaya daga kashi 22.41% zuwa 33.69% a halin yanzu a Najeriya.

4. Tsadar kayan abinci

Bayan sauran kayayyaki a kasuwa, hauhawar farashin kayan abinci ya kai 40.54% daga 24.82% war haka a Mayun shekarar 2023.

5. Farashin Dala

Lokacin da Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki a bara, ana canza dala da a kan N461, yanzu kudin Amurkan ya wuce N1400.

6. Asusun kudin kasar waje

Asusun kudin kasar wajen Najeriya ya ragu daga $35.09bn zuwa $32.74bn kamar yadda bayanai suka nuna a shafin bankin CBN.

7. Bashin da ake bin Najeriya

Rahoton Vanguard ya gaskata zancen cewa bashin da ke wuyan Najeriya ya karu daga N87.38tr zuwa N97.34tr bayan canza gwamnati.

8. Kudin ruwa a bashi

Bankin CBN ya na ta kara kudin ruwa a kan bashi har nauyin ya kai 26.25%. lokacin da Godwin Emefele ya sauka, yana kan 18% ne.

Kara karanta wannan

Matakai 10 da Gwamna Abba ya dauka wajen ayyana dokar ta baci a kan ilmi a Kano

9. Gangunan danyen mai

A watan Afrilu ne The Cable ta kawo labari cewa ana hako gangunan danyen mai miliyan 1.28 a duk rana, akasin miliyan 1.18 a bara.

10. Farashin gas

Shafin NBS ya nuna an saye kowane kilo na gas da ake girki a kan kusan N813 a tsakiyar 2023, yanzu kuwa ana maganar N1400-N1500.

Wasu ministoci Tinubu zai kora?

Shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu ya fada kuma ya nanata cewa zai kori wasu ministocinsa kamar yadda aka kawo rahotanni a baya.

Masu amfani da dandalin X sun ce wadanda ya kamata a sallama su ne irinsu ministan makamashi na kasa, Cif Adebayo Adelabu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng