Nyako, Fayose, Balarabe Musa da Gwamnonin da aka taba saukewa daga kan mulki

Nyako, Fayose, Balarabe Musa da Gwamnonin da aka taba saukewa daga kan mulki

Mun kawo maku jerin Gwamnonin da su ka taba rasa kujerar sa a Najeriya daga 1979 zuwa yanzu. A jamhuriyyar da aka fara a 1979, an sauke Gwamnan PRP daga kan mulki a Kaduna. A kwanan nan kuma an tsige Gwamnan Adamawa Murtala Nyako.

Nyako, Fayose, Balarabe Musa da Gwamnonin da aka taba saukewa daga kan mulki
A lokacin mulkin Jonathan ne aka tsige Nyako daga kan mulki
Asali: Facebook

Ga dai jerin Gwamnonin da majalisa ta taba tsigewa a Najeriya:

1. Balarabe Musa

A cikin shekarar 1981, ne majalisar dokokin Jihar Kaduna ta tsige Alhaji Balarabe Musa daga kujerar sa ta Gwamna. Jam’iyyar NPN mai rinjaye a majalisar ce ta sauke Gwamnan na PRP daga matsayin sa a karon farko a Najeriya.

2. Diepreye Alamieyeseigha

A 2005 ne majalisar Jihar Bayelsa tayi waje da Gwamna Diepreye Alamieyeseigha daga kujerar sa. An tsige Gwamnan ne a farkon Disamban 2005 bayan an same sa da laifin satar dukiyar gwamnati da almundahuna dumu-dumu.

3. Rasheed Ladoja

A farkon 2006 ne ‘Yan majalisa 16 na Jihar Oyo su kayi kukan kura su ka sauke Gwamna mai ci a lokacin Rashidi Adewolu Ladoja daga kan karagar mulki.

KU KARANTA: 2019: ‘Yan takara 23 su na harin kujerar Sanata a Kaduna

4. Ayo Fayose

Majalisar dokokin Jihar Ekiti ce ta tsige Gwamna Ayodele Peter Fayose daga kan karagar mulki a lokacin wa’adin sa na farko a Oktoban 2006. An zargi Fayose da satar kudi daga baitul mali da kuma aikata wasu laifuffuka a kan mulki.

5. Peter Obi

A Nuwamban 2006 ne aka tsige Peter Obi daga kujerar Gwamnan Jihar Anambra. An yi ta fama da rikicin siyasa a Jihar a wannan lokaci, A karshe dai Kotu ta maida Obi kan kujerar sa inda ya karasa wa’adin sa daga baya.

6. Joshua Dariye

A cikin watan Nuwamban 2006 ne kuma ‘Yan majalisar dokoki na Jihar Filato su ka tsige Joshua Dariye daga kujerar Gwamna. ‘Yan majalisar sun zargi Gwamnan da satar dukiyar baitul mali, amma a karshe Kotu ta dawo da shi kan mulki.

7. Murtala Nyako

A cikin Watan Yulin 2014 ne majalisar Jihar Adamawa ta tsige Murtala H. Nyako daga kan kujerar sa inda Ahmadu Fintiti ya dare kujerar kafin a kuma nada James Bala Ngillari. Daga karshe Kotu ta ba Byako gaskiya bayan wa’adin sa ya kare.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng