Mutane Sama da 20 Sun Mutu a Harin 'Bam' da Aka Kai Masallacin Kano

Mutane Sama da 20 Sun Mutu a Harin 'Bam' da Aka Kai Masallacin Kano

  • Ya zuwa yanzu dai mutum 21 sun mutu biyo bayan harin da wani matashi ya kai masallaci ana tsaka da sallar asubahi a jihar Kano
  • Mazaunin garin sun tabbatar da cewa an binne gawarwakin mutum 21 yayin da kuma wasu mutum 4 ke kwance a gadon asibiti
  • Wani matashi da ake zargi mai suna Shafi'u Abubakar ne ya cinna wa mutanen wuta saboda rigimar rabon gado a wani kauyen Gezewa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Rahotanni sun bayyana cewa ya zuwa yanzu mutum 21 ne suka riga mu gidan gaskiya biyo bayan harin 'bam' da wani matashi ya kai masallaci a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kinkimo namijin aikin da zai amfani mutane miliyan 30 a Najeriya

Mun ruwaito matashin da ake zargi mai suna Shafi'u Abubakar, ɗan kimanin shekara 38 ya hada 'bam' na gargajiya inda ya jefa a masallacin a lokacin da jama'a ke sallar Asubahi.

CP Usaini Gumel na Kano.
An tabbatar da mutuwar mutum 21 a harin da aka kai masallaci a Kano. Hoto: Kano Police Command
Asali: Facebook

Mutum 21 sun mutu a harin Kano

Da farko dai an ba da rahoton mutuwar mutum 10, amma adadin ya karu zuwa 21 bayan wasu daga cikin wadanda suka jikkata suka mutu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin yankin Gezawa da abin ya faru, Hamisu Abasawa, ya tabbatar da karin adadin a wata tattaunawa ta wayar tarho da gidan talabijin na Channels a ranar Talata.

Abasawa ya bayyana cewa:

"Ya zuwa yanzu mun rasa mutane 21 yayin da muka bar sauran marasa lafiya hudu a asibiti daga cikinsu akwai matasa uku da dattijo daya."

Harin ya mayar da matan Kano zawarawa

An ce akalla mutum 40 ne ke cikin masallacin lokacin da Shafi'u ya baka wutar kuma ya rufe kofofi domin hana su fita, in ji rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta tona waɗanda suka shirya zanga zanga kan rusa masarauta

Harin dai ya jefa al’ummar garin cikin zaman makoki na asarar rayukan ‘yan uwansu, kuma ya mayar da mata da dama sun zama zawarawa tare da mayar da yara marayu.

Gwamnan Kano ya magantu kan harin masallaci

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf ya bayyana takaici kan yadda wani matashi ya bankawa masallata wuta a lokacin da suke sallar Asuba a Gezawa.

Gwamna Yusuf ya sha alwashin rattaba hannu kan duk wani hukunci da kotu za ta yanke wa mai laifin wanda ya ce matashin ya kai harin ne saboda wata rigima ta rabon gado.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel