Abincin Wasu Ya Kare: Gwamna Ya Kori Shugabannin Kananan Hukumomi 16 a Jiharsa

Abincin Wasu Ya Kare: Gwamna Ya Kori Shugabannin Kananan Hukumomi 16 a Jiharsa

  • Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara ya sallami dukkan shugabanni ƙananan hukumomi 16 a jihar
  • Gwamnan ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa a daren jiya Juma'a 24 ga watan Mayu yayin da ake shirin gudanar da zabe
  • Wannan mataki na sallamar shugabannin ƙananan hukumomin na zuwa bayan hukumar zabe ta shirya yin zaɓe a watan Satumba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kwara - Gwamnatin jihar Kwara ta rusa shugabannin kananan hukumomi 16 da ke fadin jihar.

Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben kananan hukumomi a watan Satumba da muke ciki.

Gwamna Kwara ya sallami shugabannin ƙananan hukumomin jiharsa
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya shirya gudanar da zaben kananan hukumomi a watan Satumba. Hoto: AbdulRahman AbdulRazaq
Asali: Facebook

Yaushe aka sallami ciyamomi a Kwara?

Kara karanta wannan

Abubuwa sun caɓe, jami'an tsaro sun mamaye gidan gwamnatin jihar Kano

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakatariyar din-din-din na ma'aikatar kananan hukumomi, Modupe Adekeye ta fitar, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adekeye ta umarci daraktocin kula da ma'aikata daga dukkan kananan hukumomin su karbi ragamar shugabancin, cewar Daily Post.

"Daraktocin kula da ma'aikata na kananan hukumomi zasu ci gaba da jagoranci har zuwa sake yin zaben a watan Satumba."
"Wannan mataki da aka dauka ya rusa dukkan shugabannin kananan hukumomin har sai an gudanar da wani zabe."

- Modupe Adekeye

Kwara: Za a gudanar da zaben ciyamomi

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan hukumar zaben jihar ta sanya 21 ga watan Satumba a matsayin ranar gudanar da zaben.

Shugaban hukumar zabe a jihar, Alhaji Okanla Baba shi ya tabbatar da haka inda ya ce za a gudanar da zaben a dukkan kananan hukumomi 16 da ke fadin jihar.

Kara karanta wannan

"Babu mai daƙile mani hanyar abinci", Shugaban karamar hukuma ya gargadi gwamna

A shekarar 2021 ne Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya nada shugabannin kananan hukumomin 16 a jihar.

Soludo ya kori ciyamomi 21 a Anambra

Kun ji cewa Gwamnan jihar Amanbra, Charles Soludo ya kori dukkan shugabannin kananan hukumomi 21 da ke fadin jihar.

Soludo ya yi musu godiya kan irin yadda suka gudanar da ayyukan na sadaukar da kai domin ci gaban jihar.

An shafe fiye da shekaru 10 ba tare da gudanar da zaben kananan hukumomi ba a jihar Anambra sai dai nadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel