"Babu Mai Daƙile Mani Hanyar Abinci", Shugaban Karamar Hukuma Ya Gargadi Gwamna

"Babu Mai Daƙile Mani Hanyar Abinci", Shugaban Karamar Hukuma Ya Gargadi Gwamna

  • An gargadi Gwamna Siminalayi Fubara kan neman tsige shugabannin kananan hukumomi a jihar Ribas a watan gobe
  • Daya daga cikinsu da ke shugabantar karamar hukumar Ikwerre, Dakta Samuel Nwanosike shi ya yi wannan gargadi
  • Nwanosike ya ce babu wanda ya isa ya cire shi a kan kujerar har sai wa'adin da majalisar Rivers da ta ba shi ya kare

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Shugaban karamar hukumar Ikwerre a jihar Rivers, Dakta Samuel Nwanosike ya sha alwashin ci gaba da zama a kujerarsa.

Nwanosike ya gargadi Gwamna Sim Fubara kan shirin da ya ke yi a kansu inda ya ce babu mai cire shi a kujerarsa.

Kara karanta wannan

"Ina godiya Abba": Sarki Sanusi II ya magantu bayan dawowa kujerarsa

Shugaban karamar hukuma ya gargadi Gwamna Fubara kan neman tsige shi
Shugaban karamar hukuma a Rivers ya ce babu mai cire shi a kujerarsa. Hoto: Samuel Nwanosike, Siminalayi Fubara.
Asali: Twitter

Rivers: Fubara ya shirya tsige ciyamomi

Shugaban karamar hukumar ya ce shi bai aminta da wa'adin da gwamnan ya ba su na ranar 16 ga watan Yuni ba a cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ya dauki matakin ne ganin karin wa'adi da aka yi musu a Majalisar jihar karkashin jagorancin Martin Amaewhule, Punch ta tattaro.

Hakan ya biyo bayan ƙarin wa'adin da majalisar ta yi ga shugabannin ƙananan hukumomin saboda rashin gudanar da zabensu a jihar.

Shugaban karamar hukuma ya ki amincewa

Har ila yau, Nwanosike ya ce zai ci gaba da kasancewa kan kujerarsa har zuwa lokacin da wa'adinsa da majalisar ta ba su ya kare.

Ya gargadi mutanen yankin Ikwerre da kada su bari wani ya fara yunkurin cire shi daga mukaminsa na shugaban karamar hukumar.

"Saura kwanaki 23 su zo su ce za su cire ni su gani idan sun isa, ku zo ku nuna rashin bin doka. Mu doka muke bi wanda Martini Amaewhule ya tabbatar, idan kun haifu ku zo."

Kara karanta wannan

Abba ya tabbatar da korar Aminu Ado Bayero, ya sanya hannu a dokar da ta rusa su

"Idan Amaewhule ya tabbatar cewa umarnin da ya bayar shi ne in ci gaba da kasancewa a ofis, shikenan zan zauna, wannan ita ce dokar jihar Rivers."

- Samuel Nwanosike

Fubara ya yi shaguɓe ga Wike

Kun ji cewa Gwamna Siminalayi Fubara ya yi alfahari kan irin ayyukan ci gaba da ya kawo jihar Rivers a cikin shekara daya.

Fubara ya ce ayyukan alheri da ya yi a dan kankanin lokaci yafi na gwamnatoci da dama da suka shafe shekaru takwas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel