Gwamnatin Tarayya, Jihohi da Kananan Hukumomi Sun Samu Ƙarin Kuɗin Shiga a 2023 Saboda Abu 1

Gwamnatin Tarayya, Jihohi da Kananan Hukumomi Sun Samu Ƙarin Kuɗin Shiga a 2023 Saboda Abu 1

  • Gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi sun samu ƙarin kuɗin shiga daga asusun tattara kuɗaɗen shiga na tarayya FAAC a 2023
  • A wani rahoto da hukumar NEITI ta fitar kwanan nan, matakai uku na gwamnatoci sun samu ƙarin 23.56% idan aka kwatanta da 2022
  • Bincike ya nuna cewa kuɗin shigar sun karu ne sakamakon cire tallafin man fetur da shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya yi a watan Mayun bara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Tuge tallafin man fetur da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi ya ƙara yawan kuɗaɗen shigar da gwamnatoci a matakai uku suka samu a 2023.

A wata ƙididdiga da aka yi na kuɗin da asusun tattara kuɗin shiga na tarayya ya tara a shekarar, gwamnatocin sun kasafta N10.14trn a tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya raba tallafin maƙudan Kuɗi ga mutanen da matsaloli 2 suka shafa a jihar Arewa

Shugaba Tinubu.
Yadda aka samu ƙarin kuɗaɗen shiga a 2024 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, CBN
Asali: Facebook

Punch ta tattaro cewa hakan na ƙunshe ne a wani rahoto da hukumar NEITI ta fitar kwanan nan kan yawan kudaɗen da asusun tarayya ya kasafta a bara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya nuna cewa kudaden da gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi suka raba ya karu da N1.93trn a bara, idan aka kwatanta da abin da suka samu a 2022.

Dalilin da ya sa aka samu karin kuɗin shiga

NEITI ta alakanta wannan ƙarin da cire tallafin man fetur da Shugaba Tinubu ya yi tun a jawabinsa na farko a ranar 29 ga watan Mayun 2023, inda ya ce tallafin man fetur ya tafi.

Nan da nan kamfanin mai na Najeriya (NNPCL) ya aiwatar da sanarwar Tinubu, yayin da kwatsam a washe garin ranar farashin mai ya tashi daga N198 zuwa kusan N500 kan kowace lita.

Kara karanta wannan

Okuama: Bola Tinubu ya gana da gwamnan PDP kan kisan sojoji 17, sahihan bayanai sun fito

Farashin ya kuma tashi a wata guda zuwa N617/lita a gidajen mai na NNPC, yayin da sauran ‘yan kasuwa ke sayar da lita kan N660 zuwa N700 ya danganta da wurin.

NEITI ta faɗi dalilin haɗa jumullar kuɗin

Da yake tsokaci kan sabon rahoton, babban sakataren NEITI, Dakta Ogbonnaya Orji, ya ce hukumar ta yi nazari kan kudin shigar ne domin kara fahimtar da al’umma.

A cewarsa, wannan nazarin da aka saba yi a duk kwata na shekara, yana kara nuna wa ƴan ƙasa kuɗaɗen da asusun tarayya ya kasafta kamar yadda gwamnati ta sanar.

Ya ce:

"Babbar manufar fitar da wannan rahoton shi ne wayar da kai da kuma inganta yadda jama'a ke bin diddigin harkokin gudanar da kudaden gwamnati."

Yadda aka raba kuɗaɗen tsakanin gwamnatoci 3

Jadawalin kudaden shiga da aka samu ya nuna cewa Gwamnatin Tarayya ta samu N3.99trn, kashi 39.37% na jimillar kuɗaɗen, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya jero mutanen da suka koma yaƙarsa saboda matakan da ya ɗauka a Najeriya

Jihohi 36 sun samu N3.585trn wanda ke wakiltar kashi 35.34%, yayin da kananan hukumomi 774 suka raba N2.56trn kwatankwacin kashi 25.28 bisa dari.

Wani bincike ya bayyana cewa N10.143tn da aka tara a 2023 ya nuna an samu ƙarin N1.934tn ko kashi 23.56% idan aka kwatanta da N8.209tn da aka raba a 2022.

Rahoton NEITI na kwata-kwata kan kuɗin da FAAC ya tattara ya bayyana cewa tarayya, jihohi da kananan hukumomi sun karbi N1.934trn fiye da adadin da suka raba a 2022.

Gwamna ya rabawa mata talllafin kuɗi

A wani rahoton kuma Malam Dikko Radda ya rabawa mata da ƴan matan da hare-haren bindiga ya shafa tallafin N150,000 domin su fara sana'a.

Gwamnan Katsina ya kuma raba tallafin N100,000 ga iyaye mata da ƴan matan da cutar korona ta durkusar da kasuwancinsu a kananan hukumomi 34 na Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel