Jami'an DSS Sun Mamaye Fadar Sarkin Kano? Gaskiyar Abin da Ya Faru Ta Bayyana

Jami'an DSS Sun Mamaye Fadar Sarkin Kano? Gaskiyar Abin da Ya Faru Ta Bayyana

  • Hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta fito tayi magana kan rahotannin da ake yaɗawa cewa jami'anta sun mamaye fadar Sarkin Kano bayan majalisar dokokin jihar ta yi wa dokar masarautun jihar garambawul
  • Hukumar DSS ta bayyana cewa ko kaɗan babu ƙamshin dangane da rahotannin da ke yawo a kafafen yaɗa labarai cewa jami'anta sun mamaye fadar bayan
  • Daraktan hukumar DSS na jihar ya bayyana cewa an tura jami'an ne zuwa fadar domin samar da tsaro saboda ziyarar da uwargidar shugaban ƙasa za ta kai fadar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Hukumar tsaron farin kaya (DSS) a ranar Alhamis, ta musanta rahotannin da kafafen yaɗa labarai ke yaɗawa na cewa ta mamaye fadar Sarkin Kano.

Kara karanta wannan

Nadin Sanusi II: Abba ya ba korarrun sarakuna umarni a wa'adin awa 48

Hukumar DSS ta bayyana rahotannin a matsayin waɗanda babu ƙamshin gaskiya a cikinsu.

DSS ta musanta mamaye fadar Sarkin Kano
Hukumar DSS ta musanta cewa jami'anta sun mamaye fadar Sarkin Kano Hoto: @OfficialDSSNG
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta ce daraktan hukumar DSS na jihar, Muhammad Alhassan ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa DSS suka je fadar Sarkin Kano

Muhammad Alhassan ya ce hukumar ta DSS ta tura jami’anta zuwa fadar ne kawai domin samar da tsaro saboda ziyarar da uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu za ta kai wurin Sarkin.

Sai dai, ya ce daga baya an janye jami'an daga fadar saboda ɗage ziyarar da aka yi sakamakon Sarkin ba ya nan, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.

Ya ce babu gaskiya a cikin rahoton da ke cewa jami’an DSS sun mamaye fadar Sarkin ne saboda abubuwan da suka faru a majalisar dokokin jihar.

Kara karanta wannan

Jami'an hukumar DSS sun mamaye fadar mai martaba Sarkin Kano

Wane kira hukumar DSS ta yi?

Jami'in na DSS ya buƙaci ƴan Najeriya da su yi watsi da rahoton, wanda ya ce an ƙirƙiro shi ne domin haifar da ruɗani.

A ranar Alhamis ne majalisar dokokin Jihar ta soke dokar masarautun Kano ta 2019, inda ta rusa masarautun Bichi, Gaya, Karaye da Rano.

Batun tsige Sarkin Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Kano, Lawal Hussaini Chediyar Yan Gurasa ya ce a halin yanzu babu sarki ko daya a jihar Kano.

Ɗan majalisar ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan majalisar dokokin ta warware dokar masarautun Kano da tsohon gwamna, Abdullahi Ganduje ya kirkiro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel