'Ba Zai Tsinana Komai ba', Gamayyar 'Yan Siyasa Sun Soki Tinubu a Ranar Ma'aikata

'Ba Zai Tsinana Komai ba', Gamayyar 'Yan Siyasa Sun Soki Tinubu a Ranar Ma'aikata

  • Kungiyar gamayyar jam'iyyun siyasa (CUPP) ta caccaki gwmantin Bola Tinubu kan wahalar rayuwa da yan Najeriya ke ciki
  • Sakataren kungiyar ne, komared Mark Adebayo, ya yi bayanin a yau Laraba yayin bikin ranar ma'aikata ta duniya na shekarar 2024
  • Ya kuma ce kungiyar ta taya 'yan Najeriya kuka kan halin kuncin da suke ciki tare da yin kira kan matakin da ya kamata su dauka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Gamayyar kungiyar jam'iyyun siyasa ta (CUPP) ta caccaki gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu a bikin ranar ma'aikata ta duniya.

Shugaba Tinubu
Kungiyar CUPP ta ce 'yan Najeriya na shan wahala a mulkin Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Ahned Tinubu
Asali: Facebook

Kungiyar ta siffanta gwamnatin da wacce ta gaza kuma ta jefa al'ummar Najeriya cikin babban bala'i.

Kara karanta wannan

Ganduje: Kwamiti ya dauki mataki kan zargin badakala, ya fadi tsare tsaren Bincike

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa kakakin kungiyar, Kwamred Mark Adebayo, ya ce karkashin gwamnatin Bola Tinubu 'yan Najeriya sun samu kansu a cikin wahala maras misaltuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Halin da ake ciki a mulkin Tinubu

Ya ce duk da arzikin man fetur da Allah ya bawa kasar amma a halin yanzu samun mai ya zama babban al'amari a kasar wanda sai an sha wahala sosai.

A cewarsa gwamnatin ba ta da wani uzuri kan rashin samar da wadataccen mai a ƙasar kuma hakan ya jefa ma'aikata cikin zullumi.

Ya kara da cewa ba a taba samun gwamnatin da take kirkiro tsare-tsaren da suke shanye jinin talaka ba kamar gwmantin Bola Tinubu.

Ya ce tun lokacin da shugaban ya karbi mulki ya fara kirkiro damuwa ga talakawa wurin cire tallafin man fetur.

Sai kuma ga karin matsalolin tsaro da suka addabi kasar tare da hana dalibai da dama zuwa makaranta.

Kara karanta wannan

Dillalan mai sun fadi lokacin da wahalar fetur da ta mamaye Najeriya za ta kare

Haka zalika kungiyar kwadago ta koka kan yadda lamura suka dagule a kasar saboda tsare-tsaren shugaba Bola Tinubu marasa kan gado, cewar jaridar Leadership

2027: CUPP ta yi kira ga yan Najeriya

Kwmred Adebayo ya ce zaben Tinubu shi ne kuskure mafi girma da 'yan Najeriya suka yi kuma dole su gyara wannan kuskuren a shekarar 2027.

Ya kara da cewa kullum wahala ce ke karuwa a kasar gwmanti kuma sai alƙawari ta ke da bata cikawa.

A karshe kungiyar CUPP ta ce tana taya 'yan Najeriya murnar ranar ma'aikata tare da ta tayasu kuka kan halin tsanani da suke ciki.

An bada hutun ranar ma'aikata

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin Najeriya ta ba ma’aikatan Najeriya hutun rana daya domin bikin murnan ranar ma’aikata da za a yi a ranar 1 ga watan Mayu

Gwamnatin ta kuma jaddada kudurinta na ba da fifiko kan tsaro da jin dadin 'yan Najeriya, kamar yadda minista Olubunmi Tunji-Ojo ya sanar

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng