Ministan Buhari Ya Caccaki Tinubu, Ya Fadi Wani Babban Kuskure da Yake Yi

Ministan Buhari Ya Caccaki Tinubu, Ya Fadi Wani Babban Kuskure da Yake Yi

  • Tsohon ministan Buhari ya taso shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a gaba kan halin da ake ciki a ƙasar nan
  • Solomon Dalung ya bayyana cewa kuskure ne babba ɗora alhakin halin da ƙasar nwn ke ciki a kan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari
  • Dalung ya yi nuni da cewa tun da Tinubu shi ya ce a ba shi shugabancin zai iya, babu dalilin tsayawa yana ɗora laifin a kan wani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Solomon Dalung, tsohon ministan matasa da wasanni a wa'adin farko na Muhammadu Buhari, ya gaya wa Shugaba Bola Tinubu ya yi abin da ya bayyana a matsayin "mu'ujizar Legas"

A lokacin yaƙin neman zaɓensa, Tinubu ya jaddada cewa ya gina Legas a matsayin abin koyi na shugabanci nagari, sabunta ababen more rayuwa da kirkire-kirkire, ya kuma nemi a ba shi damar yin irin wannan a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tsohon gwamna ya goyi bayan Tinubu, ya fadi inda matsalar take

Dalung ya caccaki Tinubu
Solomon Dalung ya fadi kuskuren Shugaba Tinubu Hoto: Barrister Solomon Dalung, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Sai dai manufofin da shugaban ƙasar ya ɓullo da su ba su magance buƙatun ƴan Najeriya ba, sai dai sun ƙara jefa ƙasar cikin mawuyacin hali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalung ya faɗi kuskuren Tinubu

Sai dai a jerin saƙonni ta shafinsa na X, tsohon ministan ya bayyana yunƙurin da gwamnatin Shugaba Tinubu ke jagoranta na ci gaba da zargin Buhari kan ƙalubalen tattalin arziƙin Najeriya, a matsayin munafunci.

Dalung ya ce da a ce gwamnatin Tinubu ta duƙufa kan yadda ta mayar da hankali a lokacin zaɓe da kotuna don magance matsalolin tsaro da tattalin arziƙi, da an samu ci gaba sosai.

A cewarsa, zargin Buhari kan taɓarɓarewar tattalin arziƙi ba zai rage wahalhalun da jama’a ke fuskanta ba.

Yayin da yake amincewa da gazawar Buhari na cika alƙawarin "canji", Dalung ya ci gaba da cewa alhakin matsalolin tattalin arziƙin Najeriya ya rataya ne a kan gwamnatin Tinubu saboda manufofinta na riƙon sakainar kashi.

Kara karanta wannan

Tinubu vs Emefiele: Akpabio ya fadi wani babban rudani da tsohon gwamnan CBN ya haifar

Me Dalung ya ce kan Tinubu?

A kalamansa:

"Zargin #MBuhari akan tabarbarewar tattalin arziƙi ba zai iya magance matsalar tattalin arzikin da ke fuskantar al'umma ba? Shin ciniki mai yawa zai iya zama kawai mafita ga #officialABAT da tawagar tattalin arziƙinsa? Halin da ake ciki na juna biyu ya cancanci samun magani na gaggawa. Yunwa da tsadar rayuwa tana cikin matakin da ba za a iya jurewa ba.
"Ƙoƙarin canza labarin #officialABAT daga "Kada ku ji tausayina, ina neman aikin kuma na samu" zuwa zargin Buhari da # BwalaDaniel #aonanuga1956 da sauransu suke yi munafunci ne, #officialABAT ya san duk da waɗannan matsalolin, duk da haka ya kwace mulki ya gudu da shi.
"Me yasa kwatsam sai ɗora alhakin ya canza zuwa zargin Daura? Ka ƙwace mulki, oya yi abubuwan al’ajabin ka na Legas.”

Dalung Ya Goyi Bayan Sarkin Musulmi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Solomon Dalung wanda ya riƙe muƙamin ministan matasa da wasanni ya goyi bayan kalaman Sarkin Musulmi, kan halin da ake ciki a ƙasa.

Tsohon ministan ya bayyana cewa dole ne shugaban ƙasa Bola Tinubu ya nemo mafita kafin abubuwa su ƙara taɓarɓarewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel