"Tinubu Ya Dara Su", Jigon APC Ya Fadi Yadda Najeriya Za Ta Kasance a Hannun Atiku da Obi

"Tinubu Ya Dara Su", Jigon APC Ya Fadi Yadda Najeriya Za Ta Kasance a Hannun Atiku da Obi

  • Jigon jami'yyar APC, Bosun Oladele ya yi martani kan yadda Najeriya za ta kasance a hannun Atiku Abubakar da Peter Obi
  • Oladele ya ce idan da kasar na hannun mutanen biyu da yanzu Najeriya ta durkushe musamman a tattalin arziki
  • Tsohon dan Majalisar Tarayya ta yabawa Shugaban Bola Tinubu kan irin ayyukan ci gaba da ya ke kawowa Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Tsohon dan Majalisar Tarayya daga jihar Oyo, Bosun Oladele ya yi tsokaci kan ‘yan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar da Peter Obi.

Bosun ya ce idan Atiku ne ko Obi a kan mulkin Najeriya da yanzu komai ya durkuse a kasar a bangaren tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Abin da ba a taba yi ba: Dan Najeriya ya kafa tarihi a duniyar wasan 'Chess', Tinubu ya yaba masa

Jigon APC ya dira kan Atiku da Peter Obi, ya ce Tinubu ya dara su
Jigon APC ya yabawa Shugaba Tinubu inda ya soki tsare-tsaren Atiku Abubakar da Peter Obi. Hoto: Atiku Abubakar, Peter Obi, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Mene ya ce kan Atiku da Obi?

Tsohon dan Majalisar ya bayyana haka ne yayin hira da jaridar TheCable inda ya ce kwata-kwata ‘ya takarar ba su da wani hikima a tattalin arziki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce dukkan mutanen biyu ba su da ilimin gudanar da Najeriya a halin yanzu inda ya ce wannan ne karon farko da aka samu kwararre kamar Shugaba Bola Tinubu.

Ya kalubalanci jama’a su nuna masa abin da Atiku ko Peter Obi suka aikata lokacin da suka rike mukamai daban-daban.

Ya kalubalance su kan abin da suka yi

“Wadannan mutane biyu ba su da ilimin gudanar da kasa kamar Najeriya, wannan ne karon farko da aka samu shugaba masanin tattalin arziki.”
“Ka nuna min abin da wadannan mutanen biyu suka aikata lokacin da suka rike mukamai, Obi ya rike gwamnan Anambra amma babu wani abin kirki da ya yi.”

Kara karanta wannan

Yayin da ake zarginsa da sulalewa da Yahaya Bello, Gwamna ya roki Tinubu alfarma

“Atiku ya na kokarin komawa kamar tsohon shuaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, kullum sai fitar da bayanai barkatai marasa kan gado.”

- Bosun Oladele

Bosun ya ce Atiku bai tsinana komai ba lokacin da ya ke mataimakin shugaban kasa a mulkin Obasanjo a bangarori da dama a kasar.

Atiku ya magantu kan zargin cin amana

A wani labarin, Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana cewa babu wani dan Adam da zai iya ba da mulki sai Allah.

Kalaman Atiku na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake ci gaba da cece-kuce kan sakamakon taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar PDP na kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel