Uban Jami'yyar NNPP Ya Fadi Cin Dunduniyar da Kwankwaso Yake Masa, Ya Yi Masa Gori

Uban Jami'yyar NNPP Ya Fadi Cin Dunduniyar da Kwankwaso Yake Masa, Ya Yi Masa Gori

  • Shugaban jam'iyyar NNPP, Dakta Boniface Aniebonam ya caccaki Sanata Rabiu Kwankwaso kan neman kwace jami'yyarsu
  • Boniface ya koka kan yadda ya shafe shekaru 22 ya na renon jami'yyar amma rana daya Kwankwaso yana neman karbe ta
  • Aniebonam wanda shi ne ya assasa jami'yyar ya ce har gida aka roke shi ya ba Kwankwaso damar tsayawa takarar shugaban kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Wanda ya assasa jami'yyar NNPP, Dakta Boniface Aniebonam ya yi martani kan abubuwan da ya ce Rabiu Kwankwaso yake yi yanzu.

Boniface Aniebonam ya ce shirin da Kwankwaso ke yi da jama'arsa na Kwankwasiyya a kokarin kwace ragamar jam'iyyar cin amana ne.

Kara karanta wannan

Kogi: Gwamna ya sake burmawa matsala kan sulalewa da Yahaya Bello, an bukaci tsige shi

Uban jami'yyar NNPP ya zargi Kwankwaso da cin amanarsa
Uban jami'yyar NNPP, Dakta Boniface Aniebonam ya zargi Rabiu Kwankwaso da cin amanarsa. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Asali: Facebook

Zargin shugaban NNPP a kan Kwankwaso

Shugaban jam'iyyar ya bayyana haka ne a yau Juma'a 19 ga watan Afrilu a birnin Legas inda ya ce ya taimaki Kwankwaso.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ya ba Kwankwaso dama ne a cikin lalama domin ya nemi shugabancin kasar Najeriya a 2023 a cewar Premium Times.

'Dan siyasar ya kara da cewa shi kadai ya reni jam'iyyar tun daga shekarar 2002 har zuwa 2022 lokacin da Kwankwaso ya tuntube shi kan tsayawa takara.

Yadda Aniebonam ya taimaki Kwankwaso

"Buba Galadima ne ya jagoranci tawagar da Sanata Sulaiman Hunkuyi da Farfesa Sam Angai a gidana da ke jihar Anambra kan mu karbi Kwankwaso a NNPP."
"Bayan mun gama tattaunawa, na kira Kwankwaso na yi masa tambayoyi kan kudirinsa game da Najeriya, sai na ba shi dama a matsayin dan takara daya tilo."

Kara karanta wannan

Mulkin Tinubu ya dara shekaru 16 a PDP ta fuskar tsaro, Hadimin Tinubu

"Kwankwaso ba shi da masaniya kan rikicin da ke jami'yyar kawai ya yi taro tare da sauya tambarin NNPP."

- Bonaface Aniebonam

Boniface ya ce ya shafe shekaru 22 ya na renon jami'yyar amma Kwankwaso wanda ba ya cikin kwamitin amintattu ko shugaban jam'iyyar yana son kwace ta daga gare shi, cewar Daily Post.

An bukaci EFCC ta binciki Kwankwaso

Kun ji cewa Ƙungiyoyin fararen hula 45 sun rubuta wasiƙa zuwa ga hukumar EFCC domin ta binciki gwamnatin Rabiu Kwankwaso.

Kungiyoyin karƙashin ƙungiyar fafutukar tabbatar da adalci ga kowa (JA) sun buƙaci EFCC ta fara binciken mulkin Kwankwaso a Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel