Yayin da NEF Ta Yi Da-na-sanin Zaben Tinubu, Shugabannin Fulani Sun Fadi Matsayarsu

Yayin da NEF Ta Yi Da-na-sanin Zaben Tinubu, Shugabannin Fulani Sun Fadi Matsayarsu

  • Yayin da kungiyar Dattawan Arewa ta caccaki shugabancin Shugaba Tinubu, shugabannin Fulani sun bayyana matsayarsu
  • Shugabannin kungiyar Ardo a Najeriya sun nuna goyon bayansu ga Tinubu inda ta ce bata yi dana sanin zaben shugaban ba
  • Hakan ya biyo bayan caccakar gwamnatin Tinubu da kungiyar Dattawan Arewa ta yi da cewa sun yi dana sanin zaben Tinubu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugabannin Fulani a Najeriya da ake kira Arɗos sun nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu.

Shugabannin suka ce sun tallata Tinubu ne da kuma zabensa domin ya kawo karshen matsalolin da suke ciki.

Kungiyar Fulani ta bayyana matsayarta kan Tinubu bayan furucin Dattawa Arewa
Kungiyar Arɗos na Fulani a Najeriya ta ce bata yi dana sanin zaben Shugaba Tinubu ba. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Tuni da Fulani suka yi wa Tinubu

Kara karanta wannan

Ganduje: APC da PDP sun rikice, shugabanninsu sun shiga garari, an gano dalili

Shugaban kungiyar, Ardo Aliyu Liman Bobboyi shi ya tabbatar da haka a jiya Litinin 15 ga watan Afrilu yayin wani taro a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta tunatar da Tinubu kan irin alkawuran da ya yi mata yayin kamfe a zaben 2023, cewar rahoton Daily Trust.

Jagoran yankin Kudu maso Yamma, Muhammad Kabir Labar wanda shi ne Arɗon Abeokuta ya caccaki tsarin hana kiwo a birnin Abuja ba tare da samar da wani tsari ba.

Matsayar Fulani kan zaben Tinubu

Da aka tambaye shi kan matsayar Dattawan Arewa kan zaban Tinubu, kungiyar ta ce ba ta yi dana sanin zaben Tinubu ba, cewar Punch.

Ya ce kungiyar ba ta daga cikin kungiyoyi da suke dana sanin zaben shugaban inda ya ce suna tare da shi dari bisa dari.

Wannan na zuwa ne bayan kungiyar Dattawan Arewa ta ce yankin ya yi da-na-sanin zaben Tinubu.

Kara karanta wannan

Abubuwa 4 da Tinubu ya kamata ya yi domin tabbatar da tsaron makarantu a Najeriya, kungiya

Kungiyar ta bayyana haka ne yayin da ake cikin mawuyacin hali da kuma rashin tsaro musamman a yankin Arewa.

Matawalle ya kalubalanci 'yan Arewa masu mukamai

A baya, kun ji cewa karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya fusata kan yadda ake caccakar Shugaba Bola Tinubu a yankin Arewacin Najeriya.

Matawalle ya kalubalanci dukkan masu mukamai a gwamnatin Tinubu da su fito su kare gwamnati daga masu farfagandan siyasa.

Wannan ya biyo bayan caccakar Shugaba Tinubu da kungiyar Dattawan Arewa ta yi a makon da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel