"Makaho Ne Kaɗai Zai Ce Tinubu Ya Gaza" Minista Ya Maida Zazzafan Martani Ga NEF

"Makaho Ne Kaɗai Zai Ce Tinubu Ya Gaza" Minista Ya Maida Zazzafan Martani Ga NEF

  • Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle ya ce makaho ne kaɗai zai iya cewa Bola Ahmed Tinubu ya gaza a mulkin da ya fara
  • Matawalle, tsohon gwamnan jihar Zamfara ya caccaki ƙungiyar NEF kan barazanar da ta yi cewa Arewa za ta sauya shugaba Tinubu a 2027
  • Tsohon gwamnan ya ce Tinubu ya shirya yi wa Arewa ayyuka masu yawa kuma NEF ba ta da ikon yanke hukuncin wanda ƴan Arewa za su zaɓa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Duk wanda ke kallon Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya gaza ko mai rauni, ko dai makaho ne ko ɓataccen da ya kasa ganin sabuwar Najeriyar da ta kunno kai.

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya kawo mafita ga yan Najeriya kan ƙoƙarin Tinubu na kawar da ƴan bindiga

Ƙaramin ministan tsaro, Muhammad Bello Matawalle ne ya bayyana haka yayin da yake mayar da martani kan barazanar ƴan Arewa ba zasu zabi Tinubu ba a 2027.

Bola Tinubu da Bello Matawalle.
Matawalle ya ce duk mai hankali ya ga ayyukan da Tinubu ya ɗauko yi a Najeriya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Bello Matawalle
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar dattawan Arewa ta bakin mai magana da yawunta, Abdul-Azeez Suleiman ta nuna nadamar yadda yankin ya zabi Tinubu a 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NEF ta ƙara da cewa daga yanzu, Arewa za ta fi maida hankali kan haɗa kai wuri ɗaya da maslaha wajen zaɓen ɗan takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya.

Matawalle ya mayar da martani

Amma tsohon gwamnan jihar Zamfara ya bayyana ƙungiyar a matsayin "nauyin siyasa", imda ya dage cewa NEF ba ita ba ce, kuma ba za ta taba zama mai magana da yawun Arewa ba.

Matawalle ya ce shi da sauran manyan jagororin Arewa ba za su tsaya su zuba ido wasu 'tsirarun mutane' sun ɓata wa yankin Arewa suna ba.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro ya caccaki dattawan Arewa kan kalaman da suka yi game da Bola Tinubu

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da ta fito daga ofishin ƙaramin ministan tsaron Najeriya ranar Asabar, 13 ga watan Afrilu, 2024, cewar rahoton Guardian.

"Duk mun san Shugaba Bola Ahmed Tinubu GCFR ne ya lashe zaben shugaban kasa a watan Fabrairun 2023. Don haka su waye NEF da za su taɓa nasarar shugaban ƙasa har da barazanar canza shi?"
"Mafi yawan ƴan ƙungiyar sun fi sha'awar su koma gefe suna sukar gwamnati domin su yi suna. Tinubu ya shirya zubawa Arewa ayyuka masu yawa a matsayin shugaban Najeriya."

- Bello Matawalle.

Yari ya shawarci ƴan Najeriya

A wani rahoton Tsohon gwamnan jihar Zamfara ya buƙaci ƴan Najeriya su dage da yi wa Bola Tinubu addu'a a kokarinsa na tabbatar da tsaro a ƙasar nan

Sanata Abdul'aziz Yari ya ce duk wasu matakai da ya kamata, tuni gwamnatin shugaba Tinubu ta ɗauka saura kawai addu'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel