APC Ta Dauki Zafi Kan Sharrin da Aka Yi Wa Matawalle, Ta Gargadi PDP a Zamfara

APC Ta Dauki Zafi Kan Sharrin da Aka Yi Wa Matawalle, Ta Gargadi PDP a Zamfara

  • Jam'iyyar APC ta gargadi masu yada labarin cewa karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ta raba kayan abinci ga 'yan bindiga
  • Jam'iyya ta ba wadanda suka dauki nauyin yada jita-jitar da su kawo hujjoji ko su ba Matawalle hakuri kan sharrin da suka masa
  • Wannan na zuwa ne bayan yada labarin cewa Bello Matawalle ya raba kayan abinci ga 'yan bindiga a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Jam'iyyar APC a Arewa maso Yamma ta yi barazanar shiga kotu da jam'iyyar PDP a jihar Zamfara.

APC na kalubalantar PDP kan zargin da ake yaɗawa cewa karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya raba kayan abinci ga 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Rikicin El-Rufai da Uba Sani: APC ta dauki mataki kan shugabar matan jam'iyyar

APC ta tura sakon gargadi ga PDP a Zamfara kan Matawalle
APC ta shirya daukar mataki kan masu zargin Bello Matawalle da raba kayan abinci ga 'yan bindiga. Hoto: @Bellomatawalle1.
Asali: Twitter

Sakon da APC ta tura kan Matawalle

Jam'iyyar ta kalubalanci PDP da ta kawo shaidu kan zargin da ta ke yi ko kuma ta fuskanci shari'a a kotu, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yanki na jam'iyyar, Musa Mailafiya Mada ya fitar a Kaduna.

Mada ya ce su na maraba da adawa mai amfani amma bai kamata ya wuce gona da iri har da kokarin bata suna ba.

APC ta shirya daukar mataki

Ya ce PDP a Zamfara sun kware wurin batawa tsohon gwamnan jihar, Matawalle suna ba tare da hujjoji ba, cewar Channels TV.

Ya kara da cewa wadanda suka kirkiri wannan labari dole su ba Matawalle hakuri cikin makwanni biyu kuma a manyan jaridun kasar guda biyu.

Mailafiya ya ce idan har ba a dauki mataki kan wadanda suka dauki nauyin yada abin ba nan da 14 ga watan Afrilu, za su dauki matakin shari'a a kansu.

Kara karanta wannan

"Dalilin da yasa muka saki mutane 313 da muka kama bisa zargin ta'addanci a Borno," Sojoji

Gaskiya kan rabo da Matawalle ya yi

A bayan, Legit ta ruwaito muku cewa wata kafar sadarwa ta yaɗa labarin cewa karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya raba kayan abinci ga 'yan bindiga.

Kafar ta kuma ce Matawalle ya raba kayan abincin ne ta hannun hadiminsa mai suna Hon. Musa Bawa Yankuzo.

Sai dai Zamfara Newsletter ta karyata rahoton inda ta ce hakan kokari ne na batawa tsohon gwamnan suna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.