Tallafin Ramadan: Ministan Tinubu Ya Raba Shinkafa Ga 'Yan Bindiga? Bayanai Sun Fito

Tallafin Ramadan: Ministan Tinubu Ya Raba Shinkafa Ga 'Yan Bindiga? Bayanai Sun Fito

  • Wani shafin yaɗa labarai ya yi zargin cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Mohammed Matawalle, ya raba buhunan shinkafa 50 ga wasu ƴan bindiga a jihar Zamfara
  • Sai dai, an musanta wannan iƙirarin, inda aka bayyana shi a matsayin wani yunƙuri na ɓata sunan ministan daga bangaren ƴan adawa
  • Abdullahi Headmaster, wanda ake zargin ya ajiye shinkafar, ya musanta cewa yana da hannu a ciki, ya kuma yi nuni da cewa zai ɗauki matakin shari’a

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Gusau, jihar Zamfara - A kwanakin baya ne wata kafar yaɗa labarai ta bayyana cewa bincikenta ya gano cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Mohammed Matawalle, ya raba buhunan shinkafa 50 ga wasu zaɓaɓɓun ƴan bindiga a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Kungiya ta yi magana kan zargin da ake yi wa ministsn Tinubu na ba 'yan bindiga tallafin abinci

Shafin ya yi iƙirarin cewa Matawalle, wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Zamfara, ya bayar da tallafin ne ta hannun Honorabul Musa Bawa Yankuzo.

An musanta zargin da aka yi kan Bello Matawalle
Bello Matawalle ya kasance tsohon gwamnan jihar Zamfara Hoto: @Bellomatawalle1
Asali: Twitter

Sai dai kafar yaɗa labarai ta Zamfara Newsletter, ta ƙaryata rahoton, tana mai cewa wani ƙoƙari ne na ƴan adawa domin su ɓata sunan tsohon gwamnan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me aka ce kan zargin?

Kafar yaɗa labaran ta ce Yankuzo, wanda ake zargi da bayar da kayan ga ɗaya daga cikin shugabannin ƴan bindigan da ake nema ruwa a jallo, Ado Aleiro, a ranar Lahadi, 17 ga watan Maris, ya musanta zargin.

Wani na kusa da Yankuzo cikin wata sanarwa da ya aikewa Legit.ng ya bayyana cewa:

"Honorabul Musa Bawa Yankuzo ya bar ƙasar ne a ranar 5 ga watan Maris 2024 zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Umrah kuma ana sa ran zai dawo Najeriya a makon farko na watan Mayun 2024."

Kara karanta wannan

Ramadan: Murna yayin da aka fara rabon tallafin Ɗangote a jihohin Najeriya, Kano ce farko

Kafar yaɗa labaran ta kuma bayyana cewa Abdullahi Headmaster wanda ake zargi da ajiye shinkafar ya musanta zargin.

Rahotanni sun bayyana cewa yana tuntuɓar lauyoyinsa domin kai ƙarar shafin yaɗa labaran.

Matawalle ya ɗau zafi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya yi gargadi kan masu fatan juyin mulki a Najeriya.

Bello Matawalle ya umurci hukumar tsaro ta DIA da su fara farautar duk masu kiran a kifar da gwamnatin Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel