Ganduje Ya Fadi Jiha 1 Tilo da Ta Gagara Samun Ci Gaba, Ya Ce APC Za Ta Kwace Ta
- Shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya soki tsarin da jihar Anambra ke bi wanda ya hana ta ci gaba shekaru masu tsawo
- Ganduje ya ce jihar kwata-kwata bata samun ci gaba da ake zato saboda ta ware kanta madadin mannewa da Gwamnatin Tarayya
- Shugaban APC ya bayyana haka yayin taron masu ruwa da tsaki daga yankin Kudu maso Gabas kan matsalolin da suke fuskanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Shugaban jam’iyyar APC, Dakta Abdullahi Ganduje ya bayyana jihar Anambra a matsayin wacce ta gaza samun ci gaba na tsawon lokaci.
Ganduje ya ce hakan ya faru ne saboda basu tafiya tare da jam’iyyar da ta ke mulkin kasar inda ya ce APC za ta kwace jihar daga hannun APGA, cewar Punch.
Abin da Ganduje ya ce kan Anambra
Shugaban jam’iyyar ya bayyana haka ne yayin taron yankin Kudu maso Gabashin kasar kan zargin nuna musu wariya a kasar, cewar Daily Post.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce kwata-kwata jihar Anambra ba ta cikin jihohi da ke samun ci gaba a Najeriya saboda sun ware kansu.
“Kabilar Igbo ‘yan kasar Najeriya ne wadanda suke yawo a fadin kasar baki daya, jihar Anambra ta na da tasiri.”
“Amma babu wani ci gaba da ta ke samu wanda ake tsammani saboda ba ta hade da Gwamnatin Tarayya ba, wannan shi ne dalili.”
“Tun daga kan tsohon Gwamna, Peter Obi har zuwa Willie Obiano da kuma gwamnansu na yanzu, Farfesa Chukwuma Charles Soludo.”
- Abdullahi Umar Ganduje
Ya fadi yadda Tinubu ya gina siyasa
Dr. Ganduje ya ce jihar ta ware kanta yayin da wasu johohi ke faman mannewa da Gwamnatin Tarayya domin gina jihohinsu, New Telegraph ta tattaro.
“Yanzu gwamnoni su na mannewa da Gwamnatin Tarayya domin inganta jihohinsu amma Anambra ta ware kanta.”
“Kamar yankin Kudu maso Yamma da a da suke bin AD har suka dawo ACN yanzu kuma APC wanda Shugaba Tinubu ya gina, amma APGA ta tsaya wuri daya, bai kamata ba gaskiya.”
- Abdullahi Umar Ganduje
Tinubu ya roki ‘yan Najeriya
Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya roki ‘yan Najeriya da su rika siyan kayayyakin kasar domin farfado da darajar naira.
Tinubu ya ce yin hakan zai yi matukar taimakawa kudin domin ganin ta samu karbuwa da kuma inganta tattalin arziki.
Asali: Legit.ng