Tinubu Ya Roki ’Yan Najeriya Hanya 1 da Za Su Inganta Darajar Naira da Kansu Cikin Sauki

Tinubu Ya Roki ’Yan Najeriya Hanya 1 da Za Su Inganta Darajar Naira da Kansu Cikin Sauki

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya roki ‘yan Najeriya hanyar da za su bi domin taimakawa wurin inganta darajar naira a kasuwanni
  • Tinubu ya ce siyan kayayyaki daga kasar ita ce kadai hanya mafi sauki da ‘yan kasar za su ɗaga darajar naira domin inganta tattalin arziki
  • Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale shi ya bayyana haka a yau Juma’a 22 ga watan Maris yayin hira da ‘yan jaridu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayya ta bukaci ‘yan Najeria da su inganta darajar naira da kansu ba tare da saka hannun gwamnati ba.

Gwamnatin ta ce hanyar da ‘yan kasar za su ɗaga darajar Naira shi ne siyan kayayyaki da aka yi su a Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu ta gurfanar da shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah, Bodejo

Tinubu ya tura sako mai muhimmanci ga 'yan Najeriya kan inganta darajar naira
Bola Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya su rinka siyan kayayyaki daga kasar domin ɗaga darajar naira. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Wace bukata Tinubu ya nema?

Hadimin Shugaba Bola Tinubu a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale shi ya bayyana haka a yau Juma’a 22 a watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ajuri ya ce shugaban kasar ya na son hadin kan ‘yan Najeriya wurin kawo ci gaba a kasar baki daya, cewar Channels TV.

Ya ce wannan lokaci shi ya fi dacewa da za a hada kai domin kawo abubuwan da za su inganta kasar.

Matakin da Shugaba Tinubu ya dauka

“Shugaba Tinubu ya na son yin magana da ‘yan kasa a bayyane, wannan lokaci ya fi dacewa fiye da kowane lokaci domin hadin kai.”
“Ya kamata mu rika siyan kayayyaki da aka yi su a Najeriya a kowane bangare da kasuwanci a kasar.”

- Ajuri Ngelale

Ya ce wannan na daga cikin matakan da Shugaba Tinubu ya dauka domin tabbatar da ɗaga darajar Naira a idon duniya, a cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun san maboyar 'yan bindiga, Sheikh Gumi ya magantu kan afuwa ga miyagu

Tinubu ya dira kan Sanata Ningi

A baya, mun ruwaito muku cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi magana kan zargin cushe a kasafin kudin shekarar 2024.

Mai girma Bola Tinubu ya ce duk wadanda ke zargin an yi almundahana a kasafin kudi ya tabbata ba su da ilimin lissafi ko kadan.

Wannan na zuwa ne bayan Sanata Abdul Ningi daga jihar Bauchi ya yi zargin cushen N3.7trn a cikin kasafin kudin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel