Hantar Gwamnan Ta Kaɗa Yayin da Ganduje Ya Faɗi Jiha 1 da APC Za Ta Ƙwace a 2025

Hantar Gwamnan Ta Kaɗa Yayin da Ganduje Ya Faɗi Jiha 1 da APC Za Ta Ƙwace a 2025

  • Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce lokaci ya yi da jihar Anambra za ta rabu da APGA ta dawo hannun APC
  • Ganduje ya ce Anambra ta cure wuri ɗaya ta gaza samun ci gaba sabida jam'iyar APGA mai mulki ta kasa matsawa gaba
  • Tsohon gwamnan jihar Kano ya yi ikirarin cewa APC za ta kwace jihar Anambra ta hannun Sanata Ifeanyi Ubah a 2025

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Nnewi, jihar Anambra - Shugaban jam'iyyar All Progressive Congress (APC) na ƙasa, Abdullahi Ganduje ya ce jam'iyya mai mulki za ta ƙarɓe jihar Anambra daga hannun APGA.

Ganduje ya ce jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ta gaza samun ci gaba a siyasa shiyasa jihar Anambra take wuri ɗaya, jiya a yau.

Kara karanta wannan

Ganduje ya fadi jiha 1 tilo da ta gagara samun ci gaba, ya ce APC za ta kwace ta

Shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje.
"Lokacin Murna Ya Zo" Ganduje Ya Hango Jihar da APC Za Ta Karbe a 2025 Hoto: Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Facebook

Ya ce jihar da ke Kudu maso Gabashin Najeriya ba ta samun ci gaban da ake tunani ne saboda ta raba kanta da cibiyar gwamnati ta ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Ganduje ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a wurin taron masu ruwa da tsakin APC na shiyyar Kudu maso Gabas.

Wannan taro ya gudana ne a Nnewi ta jihar Anambra ranar Jumu'a, 22 ga watan Maris, 2024.

A rahoton The Nation, Ifeanyi Ubah da APC sun shirya wannan taro ne domin wayar da kan mambobin jam'iyyar da mazauna Anambra cewa ba a nuna wariya ga Kudu maso Gabas ba.

APC za ta karɓe mulkin jihar Anambra

"Lokaci ya yi da zamu sha shagali kuma muna fatan cewa APC za ta kwace jihar Anambra ta hannun Ifeanyi Ubah. Anambra ita ce zuciyar shiyyar Kudu maso Gabas.

Kara karanta wannan

Okuama: Shugaban majalisar dattawa ya faɗi waɗanda yake tunanin suna da hannu a kisan sojoji 17

"Kuma wannan shi ne lokacin da ya kamata jihar ta haɗe da ciyar gwamnati a inuwa guda domin ta farfaɗo, zamu tabbata jihar Anambra ta manne da APC mai mulki.
"Ba bu sauran barazana, Anambra tana da muhimmanci a tattalin arzikin Najeriya kuma ya zama wajibi ta manne da cibiyar gwamnatin tarayya."

- Abdullahi Ganduje.

Abba ya gana da ministan Tinubu a Kano

A wani rahoton na daban Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi bakuncin ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris a gidan gwamnatin jihar Kano.

Ministan ya kai ziyara ta musamman da Gwamna Abba Kabir ne a fadar gwamnati da ke birnin Kano da safiyar ranar Jumu'a, 22 ga watan Maris, 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel